Na nemi bankina su tura min 'account statement' daga January zuwa June (first half ta 2024) na ga yadda nake gudanar da shige da ficen haƙƙina, sai na ji kamar na ɗauki bulala na zane kaina da kaina.
Da na duba 'screentime' na waya don bin diddigin yadda nake amfani da wayoyin hannuna, a nan ma na ji kamar na zane kaina, musamman 'social media' tana buƙatar 'detoxification' da 'yan lokuta.
Na duba MyMTN, na ga subcriptions da ƙiran wayar da na yi a 'first half', nan ma akwai buƙatar na sake zama.
Na duba 'daily routines' nawa, da yadda nake gudanarwa da lamurana na yau da kullum da abubuwan da cimma a first half, nan ma ina buƙatar ƙara wa kaina discipline.
Ni ya kamata na fara yi wa kaina hisabi, na duba alaƙa ta da Ubangijina, ibada, mu'amalata da mutane, aiyukana, kasuwancina, yadda nake gudanar da lokaci da kuɗaɗena... tun kafin ma wani ya dube ni ya ce, kana abu kaza ba daidai ba.
Ni ya kamata na duba wuraren da nake da weakness na ƙara strengthing kaina tun kafin wani ya gano raunina. Ni ya kamata na zauna, na yi nazarin shin rayuwar da nake yi a yanzu ta yi daidai da manufa da burin da nake son cimma a rayuwa ko kuwa? Ni ya kamata na sake zama da nazarin rayuwata domin kaina nake yi wa rayuwar nan ba kowa ba, a duniya da lahira.
Shi ya sa Sayyadina Umar ke ce wa: "حاسبوا أنفسكم قبل أن تحاسبوا وزنوا أنفسكم قبل أن توزنوا، فإنه أهون عليكم في الحساب غدا أن تحاسبوا أنفسكم اليوم، وتزينوا للعرض الأكبر يومئذ تعرضون لا تخفي منكم خافية".
Ma'ana: "Ku yi wa kanku hisabi tun kafin a yi muku hisabi, ku riƙa auna kanku (tun) kafin a auna ka, zai fi sauƙi a gare ku a wajen hisabi gobe idan kun yi hisabi da kanku a yau..." (ighathatul Lahfan 1/145).
#AliyuMAhmad #AliMotives #RayuwaDaNazari
0 Comments