Akwai Laifinka!


Zai yi wahala, kafin wani ya wulaƙanta ba kai ne ka fara wulaƙanta kanka ba.

Zai yi wuya, kafin wani ya yaudare ka ba kai ne ka fara yaudarar kanka ba.

Matsalolinmu da yawa suna farawa da kanmu ne, amma sai mu zargi wasu mutane, duk da wani lokacin a kan samu wasu mutane su yi mana kutse ba tare da gudunmawarmu ba.

Misali,

• Kana matashi, kana son yarinya, duk wasu red flags 🚩 na ta nuna ba kai take ƙauna ba ta nuna maka, amma ka nace, ka manne; da tafiya ta yi nisa, ta bayyana maka ƙarara ba son ka take ba; sai ka dawo kana zaginta ta yaudare ka, ta wulaƙanta ka. Me ya sa ba ka duba matsalar ta fuskarka ba? Me ya sa ka yi naci, ba ka haƙura ka ɗauki soyayya a matsayin jarrabawa ba?

• A wajen aiki an gindaya ƙa'idoji, kai kuma sai ka bi ka saɓa. Aka ƙira ka domin ya ɗau mataki a kanka sai ka ce an ci zarafinka. Me ya sa kai ba za ka reflecting da matsalar daga ɓangarenka ba?

• Gwamnati ta yi dokar tuƙi, sai kuma sai ka saɓa; 'yan road safety (FRSC) suka kama ka, suka yanka maka tara, sai ka koma gefe kana cewa azzalumai ne, me ya sa kai ba za ka duba laifin da ka yi ba?

• Mutane suna ce wa kana da girman kai, ƙazanta, shisshigi, iya yi... kafin ka ce ana ɓat ka ko yi maka mummunar sheda, ka fara duba kanka, shi hakan kake, sai ka gyara, ko kuma sharri ne, sai ka kauda kai?

Mu 'yan Adam ne, muna iya kuskure, mu gaza a wasu fuskoki. A duk lokacin da aka sami akasi, ka fara nazari, shi ni mene ne gudunmawata aka sami wannan akasin? Ina da laifi a ciki? Idan akwai gudunmawarka, sai ka gyara a gaba.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments