Ƙuduri


Idan ina son abu, ba ce wa zan yi ina son wannan, this is my dream, bla, bla... ba kawai, nazari zan yi ta ya za a yi na mallaki wannan abun, ta ya zan cimma wannan ƙudurin nawa.

Zan riƙe sababi, 
Zan kuma yi addu'a,

Zan riƙe Allah ya taimake ni na cika burina. Idan ba alheri ba ne, Allah ya canja min da wanda ya fi shi alheri.

Ka ga kwamfuta kana so,
Ka ga mota kana so,
Ka ga gida kana so,
Ka ga sutura kana so,
Ka ga wani 'skill' kana son koya...

Kullum da "wow!" za ka tsaya, ko kuma za ka kama sanadin da zai sadar da kai ga wannan ƙudurin? Ka zama kamar Engr. Adam Muhammad Mukhtar , shekarar da ta gaba a 11th November, 2023 ya rubuta ƙarara a Facebook ce wa yana son zuwa Umrah a wannan shekarar kuma a 5th February, 2024 burinsa ya cika. Wataƙila a lokacin da ya yi wancan ƙuduri bai shirya ba, ya dai yi niyya kuma Allah ya taimake shi.

Ka zama kamar Muhammad Auwal Ahmad lokacin da zai fara StackPlaza da Flowdiary , mentor sa ya ce masa, ka tsara, ka fara, ka gina long term project daga nan zuwa shekara 5, yanzu ya fara, daga 2022 zuwa yau ya nisan tafiyarsa?

Ka zama kamar Mallam Murtala Kazaure da a 17th June, 2020 yake da ƙudirin idan ya zama gwamna Jihar Jigawa zai inganta ɓangare fasahar zamani (IT), a yau ya fara da zama Special Assistant (S.A.) na Gwamna kan fannin IT, tun November, 2023 zuwa yau yana aiki bisa wannan ƙudurin.

Idan nan da kwana 10 kana da buƙatar ₦50k, kuma ka san a irin nemanka, ta iyu ka iya tara ₦50k kafin lokaci, ko ƙasa da haka, ko fiye. Idan fa ka yi ƙuduri, kuma ka sanya wannan manufar a raika, a ƙalla ko ba ka tara ₦50k a kwana 10 ba, a ƙalla dai za ka kusa kai wa inda ka nufa fiye da a ce ba ka da wani ƙuduri.

Malam! 

Tsuntsu shi ne ake kwatance da 'tawakkali', amma ka san duk safiyar Allah sai ya yi 'hustle' ya fita ya nema, kuma yana samu.

لو أنكم تتوكلون على الله حق توكله لرزقكم كما يرزق الطير، تغدو خماصاً وتروح بطاناً

Ubangiji ﷻ yana shiga lamarun wanda ya shirya, ya dage, ya jajirce: "والذين جاهدوا فينا لنهدينهم سبلنا"

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments