BA A HAƊA GUDU DA SUSAR ƊUWAWU


Kana matashi, shekarunka ƙasa da 18 zuwa 25/30, a kan me ya kamata ka fi maida hankali a yanzu?

GINA KAI

Ka tsaya ka gina kanka, ba wanda zai gina ka sai dai ya tallafa ma ka wajen gina kanka.

Iyayenka da za su biya maka 'school fees' tallafi ne, kai ne za ka zage ka yi karatu, ka gane karatu, ka sami sakamako mai kyau. Idan ka yi wasa, kai ka yi asara. Sun yi iya abin da za ma na ba ka 'scholarship'. Yara nawa ne har 'abroad' iyayen sun kai su sun ƙi tsayawa su yi karatun da kyau, sai dawo da su gida aka yi?

Mai gidanka da zai koya maka aiki (skill) don ka kware, taimaka maka kawai zai yi, kai ne za ka maida hankali ka koya. Idan ka yi wasa kai za ka yi wa kanka asara. 

KA RAYUWA DA MANUFA

Saboda sabuwar 'balaga' tana motsa ka, babu tarbiyyar da za ka yi wa kanka face nesanta kanka daga harka mata, da sunan soyayya ko biyan sha'awa.

Da lokacinka,
Da kuɗinka,
Da wannan fikira tsara 'yan matan...

...ka yi 'investing' ɗinsu wajen gina kanka. Duk wata alaƙa da aiki da za ka yi ka riƙa lura da 'outcomes', da me zai amfane ka? Uwar me soyayya za ta amfanar da kai a yanzu ko ɓata lokaci?

Idan akwai mutanen da za ka farantawa a lokacin fafutukar gina, IYAYENKA ne domin neman albarka. Ba 'yan matan da idan kuka sami saɓani za su maka "ME KA TAƁA MIN?" ko "NI NA SAKA KA?" ba.

KADA KA YI GAGGAWA

Kada ka takurawa kanka sai ka sa sutura kala kaza, ka riƙe wayar hannu (phone) irin ta wane, ka sayi abin hawa ko cin abincin 'yan gayu. KAI! Ka rayuwa daidai da matsayinka.

Kowanne sisi da kobo da da za ka kashe ka duba manufar kashe kuɗin. Me ya sa sai wayar ₦500k zan riƙe? Me za ta kawo min? Wayar ₦50k ba za ta biya min buƙatu ba? 

A shekarunka ba lalle ka tara abin duniya irin na ɗan shekaru 45 - 60 ba, ka san yaushe suka fara gwagwarmaya? Akan me sune kawai madubin rayuwarka kana ɗan ƙasa da shekara 30 ko 25? 

KA RABA KANKA DA MAƘIYANKA

Maƙiyanka ba wasu mutane ba ne dake kusa ko nesa da kai, ZUCIYARKA ita babbar abar da za ta dankwafar da kai idan ka biye mata:

• Ka cire kasala, lokacin fafutuka ba lokacin hutu ba ne (namiji ne kai),
• Ka nisanci mata da sunan soyayya,
• Kada ka haɗa hanya da shaye-shaye,
• Ba ruwanka da gasa da abokai,
• Ka guji dogon buri,
• Mai koyo ne kai a yanzu, ka guji nuna gwaninta da kamala (perfection),
• Ka kiyaye fuskarka daga ƙarya, cin amana, girman kai da tsaurin ido.

Ka yi aiki tuƙuru,
Ka kuma jira lokaci!

✍🏿Aliyu M. Ahmad
8th Shawwal, 1445AH
17th April, 2024CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments