Cin Amana Ne!
• Cin amana ne! Idan kana WAYA ko ZAUNE da wani ka naɗi muryarsa (recording) ba tare da saninsa ko amincewarsa ba, har ka iya yaɗawa (sharing) ga wasu.
• Cin amana ne! Ka buɗe muryar mutum 'handsfree/loudspeaker' ba tare da sanin abokin yin wayarka ba, a cikin jama'a.
• Cin amana ne! Yin SCREENSHOT na chat da kuka yi da wani/wata ka tura ko nunawa wasu ba tare da izini ko sanin ɗayan ba.
A lokacin da kuke magana da wani shi ya aminta da kai, ya saki baki yana faɗar magana zuciyarsa ɗaya, kai kuma kana yi da takatsantsan saboda ka san abin da kake, na naɗar muryarsa (recording), ko screenshot na chat, musamman abin da yake sirri ne, ko abu maras kyau, da zai iya ɓata abokinka.
Gulma, annamimanci, ha'inci da cin amana sun zama kamar ba komai ba a SOCIAL MEDIA ta hanyar naɗar muryoyi ko chats na mutane, kuma laifuka ne MANYA-MANYA (Kaba'ira) cikin ADDINI, masu hatsari a nan duniya da lahira, da ake yi a kullum. Hakan na iya 'raba aure' ko 'soyayya' ko 'haddasa gaba tsakanin mutane/abokai/aminai biyu' duk saboda annamimanci da ha'inci na mai naɗewa ko screeshooting na sirri da suka yi da wasu a chats ko a ƙiran waya.
Imam At-Tirmidhi (1959) da Abu Dawud (4868) sun ruwaito Hadisin Jabir ɗan Abdillah (RA) cewa; Manzon Allah ﷺ Ya ce: "Idan wani mutum ya so magana da wani sai ya ɗan waiwaiya (don ya tabbatar ba mai kallonku ko jinku), duk abin da zai faɗa ma amana ne."
Ina ga a private chat ko ƙiran waya?
Mai cin amana, yana ɗaya daga cikin nau'in mutune biyu da suna hawa siraɗi ƙugiya zata fincike su ta cilla su wuta (Allah Ya mana tsari), kamar yadda Abdullahi bin Mas'ud (RA) ya bawa Murrah amsa da ya tambaye shi Tafsri/ma'anar ayar "وإن منكم إلا واردها كان على ربك حتما مقضيا" cikin Tirmidhi. Cin amana alama ce ta munafurci (Muslim 58). Mai cin amana ba zai shiga aljanna ba.
Ubangiji na yafe laifukan zina, shirka, da sauransu; saboda wannan tsakaninSa ne da bawa; amma baya yafe laifukan cin amana da ha'inci saboda wannan tsakanin bawa ne da bawa (mutum da mutum). Tuban irin wannan kuwa, ko dai ka nemi yafiyar wanda ka ciwa amana (ta irin wannan hanya) a nan duniya, ko kuma in an je Alƙiyama a biya shi da aikin alkhairin da ka yi a duniya ko kuma a rage zunubinsa a jibga ma, a kuma kaɗa ka wuta (Bukhari, 2449) Allah Ya mana tsari.
Allah Ya bamu ikon kiyayewa!
(c) Aliyu M. Ahmad
22nd Muharram, 1443AH
30th August, 2021CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #FasaharZamani
0 Comments