Ni ma na fi ba wa mutane shawarar su BUILDING ORGANIC COMMUNITY fiye da siyan page masu followers da yawa, sai dai idan don wata manufa ne ake son page mai followers da yawa (BA INA KASHE WA MASU SIYAR DA SHAFI KASUWA BA NE, su ma suna taimakawa a wurare da yawa don cimma manufar ƙirƙirar shafuka daidai da buƙata).
Ɗazu na yi post kan wani ya sa a nema masa page mai followers 40k, 40k? Eh! Akwai dalilin da ya sa yake neman mai 40k followers zuwa sama, akwai manufar da yake son cimma.
(Wani) Siyan pages mai followers yana rage engagement quality, algorithm impact... saboda PAGE FLIPPING, followers da aka sayi pages ba don sabon contents da za a wallafa suke bibiyar shafin ba, babu relevancy. Wani yana ga content saɓanin na baya (page flipping) zai unfollowing shafin, ya fece.
Yawancin shafukan da ake siya irin waɗanda ake ɗora hoton 'yan film ne, 'yan mata, contents na barkwanci... don jawo hankali mutane (an fi son nishaɗi to). Za a sami akasi idan shafin ka mayar na abin addini ko karatu, ko promoting business da ba shi da alaƙa ba manufar shafin ta asali.
Akwai waɗanda sana'arsu ce ma rainon shafi idan ana nema su sayar (PAGE BROKERS), kuma kyakkyawar kasuwa ce, ka siya idan kana da wata manufa da kake son cimma wa. Ba iya pages, har reactions akwai masu sayar wa (ENGAGEMENT MANIPULATORS) ta hanyar MEMA strategy (manipulative engagement metrics).
Ko za ka sayi shafi sai ka sami kwarraren metric analyst ya duba demography na followers (audiences), GREEN QUALITY (lafiyar shafi) domin idan shafi yana da restriction za ka sha baƙar wahala. Za ka iya sayan shafin mai 1 million followers amma idan ka yi post ko 10 reactions ba za ka samu ba, saboda RED QUALITY, hala shafin ya saɓa wani community standard an saka shi a shadow blinding, ya shiga restriction na abubuwa da yawa.
Idan kana gaggawar gina shafi, investment ake, mafi araha influencer collobration, akwai wani shafi Fitila Impact Hub da suka yi wannan tsakanin 29th June zuwa 1st July, 2024. Yanzu da za su yi post 1, ta iyu reactions na 10% na organic followers nasu 80 - 100 cikin 800 followers. Amma sai ka ga shafi mai followers 50k, 80k, 100k sun yi post ba reactions ko ɗaya, kuma idan ka duba engagement metric ba shi da yawa saboda page flipping, impact na algorithm a kan shafi zai rage masa visibility.
Hanya ta biyu kuma, PROMOTION, ka riƙa biyan kuɗi Facebook suna boosting maka contents misali TRT Hausa, ko optimization, ko samar da contents (a hoto ko video) masu quality, engaging following a shafinka su riƙa faɗar ra'ayinsu misali BBC Hausa da suke samar da engagement questions kusan kullum, mene ne wannan? Me ake riƙa wannan? Ƙara wannan karin maganar da sauransu.
✍🏻Aliyu M. Ahmad
3rd Muharram, 1446AH
9th July, 2024CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives #FasaharZamani #SocialMedia
0 Comments