Sadaka mafi alheri ita ce,
Ka fara da kanka,
Ka kyautata wa iyayenka,
Ka kyautata wa iyalanka.
Kada ka san iyayenka na buƙata, sai kuma ka je kana kai wa sadaka da tallafi wani wuri. Kada iyalanka (a gida) ka san suna buƙata, ka tafi kana kai wa a wani wuri. Kada 'yan uwanka da makwaftanka suna cikin tsananin buƙata a ji kana bada sadaka a nesa.
An karbo daga Abu Huraira رضي الله عنه ya ce:
Wani mutum ya zo wurin Annabi Muhammad ﷺ ya ce, "Na hallaka!" Annabi ﷺ ya ce, "Me ya same ka?" Ya ce, "Na yi jima'i da matata ne yayin da nake azumin watan Ramadan." Annabi ﷺ ya tambaye shi, "Shin, za ka iya 'yanta baiwarka?" Ya ce, "A'a". Annabi ﷺ ya sake tambayar shi, "Shin, za ka iya yin azumi na watanni biyu a jere?" Ya ce, "A'a". Annabi ﷺ ya tambaye shi, "Shin, za ka iya ciyar da miskinai sittin?" Ya ce, "A'a". Annabi ﷺ ya yi shiru. Sai aka kawo wa Annabi ﷺ kwando cike da dabino. Annabi ﷺ ya ce, "Ina mai tambaya?" Ya ce, "Ga ni". Annabi ﷺ ya ce, "Ka ɗauki wannan ka bayar sadaka". Sai mutumin ya ce, "Ya Manzon Allah, babu wani da ya fi mu buƙata a cikin Madinah". Annabi ﷺ ya yi dariya har haƙoransa na gaba suka bayyana, sannan ya ce, "Ka ɗauka ka ciyar da iyalinka".
Wannan yana cikin Bukhari hadisi mai lamba ta 1936 da Muslim hadisi na 1111.
• Ubangiji ya yi umarni da a kyautatawa iyaye,
• Ciyar da iyalanka (matanka da 'ya'yanka) sadaka ne,
• Sai yan uwa, makusanta,
• Sai makwafta, da kuke zaune a unguwa ɗaya
• Sai miskinai (masu buƙata ta musamman) da fakirai (talakawa), marayu da zawara, da masu hidimtawa addinin Allah.
Wannan yana daga cikin tarbiyyar bayar da sadaka, tallafi ko taimako daga Alƙur'ani da Sunnah, cikin Baƙara aya ta 215:
يسألونك ماذا ينفقون قل ما أنفقتم من خير فللوالدين والأقربين واليتامىَ والمساكين وابن السبيل
Abu Huraira رضي الله عنه ya ce, wani mutum ya zo wurin Annabi ﷺ ya ce, "Ya Manzon Allah, wane irin sadaka ta fi girma?" Sai Annabi ﷺ ya ce, "Sadaka ga wanda ya fi kusa da kai, sai wanda yake kusa da kai" (Bukhari, Hadisi na 1462; Sahih Muslim, 997).
A wani hadisin na Jarir bin Abdullah رضي الله عنه ya ce: "Mun kasance a wurin Annabi Muhammad ﷺ sai ya ce: 'Duk wanda yake da halin da zai ciyar da wasu, sai ya fara da kansa, sai iyalansa, sai 'yan'uwansa, sannan sauran mutane" (Muslim, 1034).
A cikin Sunan Abu Dawud, hadisi na 1691 kuma, Abu Huraira رضي الله عنه ya ce: Annabi ﷺ ya ce: "Mafi alherin sadaka ita ce wadda aka ba 'yan'uwa (masu buƙata) yayin da suke cikin buƙata, kuma ka fara da waɗanda suka fi kusa da kai."
Waɗannan nassoshi suna nuna muhimmancin fara ba da sadaka ga iyalai, makusanta, makwabta, da kuma miskinai kafin komawa ga sauran mutane.
✍🏻Aliyu M. Ahmad
9th Dhul-Hijjah, 1445AH
15th July, 2024CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments