Kwaila


Kwaila ta ɗauka wanda zai ƙira ta a waya, su shafe 3hrs, 5hrs, 7hrs... a kullum suna waya shi ne mai son ta da gaske. Shi ya sa mai zaman banza ko buga-buga, sai ya yi nasara a kan soyayyar wanda ya tsaya da ƙafafunsa, saboda shi yana busy da aiyukan gabansa.

Idan kana soyayya da ita, dole ka bar uzurinka masu muhimmanci ka ba ta kulawa, a yi ta waya, ba ta damu da ko za ka disappointing na kowa ba, ba ta damu da aikin da za ka maida hankali, da shi ne za ka kawo kuɗin aurenta.

Bro! Kada ka yi kuskure, ba kwaila ba, ko cikakkiyar budurwa ce ya zamana lokacin aikinka za ka katse saboda uzurinta, musamman don yin hira a waya kawai, ba ka ma gajiya?

ENTAILMENT

Idan yarinya tana da irin wannan hali idan ma ba ka mata ba, za ta nemi wani ya yi mata. Za ta fitini kanta:

Ita a dole sai ka bata lokacinka,
Ita a dole sai ka kula da ita, 
Ita a dole sai ka nuna ka damu da ita, 
Ita a dole sai an yi kishinta.

Misali, 

1. Freeloading

Akwai wacce a ranta tana jin ajinta ne sai ka kashe mata kuɗi (haka kawai), tana jin idan ta zo maka da buƙata kana rawar jiki za ka biya mata, ba za ka kwafsa ta ba. Wannan shi ake ce wa 'FREELOADING'. 

In faɗa maka, tun da ba dole ba ne, idan ba ka mata, ina tabbatar maka za ka gan ta da abun, ta mayar da buƙatar wajen wani, misali; anko, ko wasu accessories.

2. Jealousy Induction

Haka kawai za ta sanya ka kishi, don ta nuna ta isa a yi kishi a kanta. Misali, idan kana da 'appointment' da ita na son ganin ta, kafin ka zo, za ta ƙara bawa wani dama ya zo kafin kai, ko ya zo bayan ka zo, don ka ga wani na bibiyarta kawai ka nuna kishi.

Ko kuma ta ƙira wani a waya kafin haɗuwarku, shi kuma ya yi ta ƙira, taƙi ɗagawa saboda kuna tare. Entailment ne na son a cusa maka kishi, sai ka nuna kana kishinta, 'emotional manipulation' ne kawai, ka dake ka nuna ba ka damu ba.

3. Clinginess

Kana aiki, tana san kana wajen aiki, amma za ta dame ka da ƙira, ƙira, chats, SMS... Idan ba ka bi ba ta yi fushi, ko shagwaɓa. Ita tana ji a dole sai ka bar komai duk muhimmancin abu ka ba ta lokacinka, wannan zai sa ta ji tafi komai muhimmanci a wajenka.

Su ma masu waɗannan halayyar ba su san suna yi ba, unconsciously suke yi yawanci, ya zama ɗabi'a.

-----------

Idan ina karatu, na kan ce, kuskure ne matashi ya ɓata lokaci wajen soyayya, maimakon ya investing emotions da lokacinsa don gina kai a 20s - 30s. Wani lokacin kuma na kan ce, kuskure ne matashi ya yi asarar ɗinbin ire-iren waɗannan darussa na 'dark psychology' don koyon zaman duniya.

✍🏻Aliyu M. Ahmad
3rd Dhul-Hijjah, 1445AH
9th June, 2024CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments