Idan ba za ka iya sayan kaya 'yan kanti (boutique) ba, ka je gwanjo ka zaɓa, riga da wando masu kyau, ka fito fes.
Idan ba za ka iya sayan nama, ko kifi, ko kwai ba, ka yanka cabbage 🥬 da albasa.
Idan kuɗin guga (ironing) ya yi maka tsada, naɗe kayanka tsaf, ka zaune a kansu ka yi 'yar Madina.
Wata ta ce ba ta son ka, share ta ka nemi wata, daidai da kai. Kada ka sanya wa kanka damuwa.
Abin da mai iPhone zai yi na ƙiran waya, chatting, browsing... kai ma za ka iya yi da Tecno, Infinix dake hannunka.
Ba za ka iya affording zuwa formal school ba, kada ka zauna haka babu ilimi, ka nemi ilimi a YouTube, Coursera, Udemy, Alison... kyauta da za su inganta maka rayuwa.
Idan akwai da wadata, ka more. Idan babu, ka daidaita rayuwarka da yanayi. Ba takurawa kai, babu kwaikwayo da gasa.
Komai na rayuwar nan, ka yi daidai da kai, kanka kake yi wa rayuwa ba kowa ba. Ba ruwanka da dogon buri, hangen ni'imar wani ka manta taka, hassada ko cin basussuka don ka ɗorawa kanka abin da ya fi ƙarfinka.
✍🏻Aliyu M. Ahmad
26th Dhul-Qidah, 1445AH
3rd June, 2024CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments