Ya kamata a kullum ka tashi da safiya, ya kasance akwai wani ƙuduri da kake son cimma a yau, daga tashinka daga bacci, zuwa lokacin da za ka koma bacci, ka yi duk mai iyuwa ganin ka cimma wannan ƙuduri.
Haka a wannan SATI mai shigo, daga Litinin (ko Lahadi) zuwa cikar sati, kana da wani ƙuduri da kake son cimma a wannan satin.
Haka a WATA, daga farko wata zuwa ƙarshensa. Haka a SHEKARA, daga January zuwa December (ko daga Muharram zuwa Dhul-Hijjah). Kada ka taɓa zama kara zube, ba ka da wata manufa ko ƙuduri, kana tsammani wani 'magic' zai kasance a rayuwarka haka kawai.
Gwamma ka sawa rayuwarka manufa da ƙuduri, ka gaza cimma ƙudurinka, da a ce ka zauna kara-zube. Ko ba ka cimma ƙudurinka ba, a ƙalla za ka koyi darussa da dama, kuma za ka fi jiya ci gaba a rayuwarka. Bal! Ba wani abu da wani ɗan Adam zai yi da ba za ka iya ba, sai dai idan ka ɗauko abin da ya fi ƙarfinka, ko ka gaza samun hanyar gudanarwa.
Sanya manufa a rayuwa na ɗaga cikin darussan da ya kamata mu ɗauko daga rayuwar makaranta. Cikin wasu 'yan shekaru aka tsara mana son cimma wata manufa ta gina kai da karatu, kwarewa da kuma tarbiyya.
• A kowacce rana akwai jadawali.
• A kowanne sati akwai jadawali.
• A kowacce semester/term akwai abin da ake son cimma.
• A cikin zangon karatunka akwai abin da ake son ka zama, likita, ko lawyer, linguist ko educationist, engineer ko economist...
Sanya wannan manufar ya sa a kai ga nasara, har aka samar da sabbin samfurin 'yan Adam da za su amfanar da kansu, su amfanar da al'umma.
Wacce manufa ka sanya wa kanka a yau? Wane project kake da shi yau? Ko wanki da guga za ka yi? Wacce manufa kake da ita a sati mai shigo? Tara kuɗi? Ta wacce hanya? Ko biyan bashi? Karance littafi? Aiwatar da wani aiki/project? Kafin shekarar nan ta ƙare, me kake son cimma? Gina gida? Sake abin hawa? Aure? Sauya aiki? Me kake son cimma rayuwa gaba ɗaya kafin mutuwa?
Wani hikima, Benjamin Franklin (1701 -1790) kan ce, "wanda ya gaza ya yi tsari, ya tsara faɗuwa" (he who fails to plan, he plans to fail). Ubangiji ﷻ kuma ya faɗa mana, cikin Alƙur'ani Mai girma, Al-Anƙabut, aya ta 69:
والذين جاهدوا فينا لنهدينهم سبلنا وإن الله لمع المحسنين.
✍🏻Aliyu M. Ahmad
18th Dhul-Qidah, 1445AH
26th May, 2024CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments