Ana Gara Tunanin Matasa


Ba fa lalle ne duk abin da wani ya yi ya samu nasara, idan kai ma ka yi za ka yi nasara ba. Wani idan ya yi rawa aka ba shi kuɗi, wani duka zai ci. Just do what will work for you, ko mene ne idan zai rufa maka asiri.

Duk wata harka da wani zai shiga ya yi nasara a shekaru kaɗan, 2, 3 ko 5; akwai wanda ya fi shekara 10 ko 20 a wannan harkar bai yi nasara ba. 

Na yarda da maganar Engr. Abdulrazak Rogo duk an bi an rikita matasa, illar information overload kenan. Da yawanmu matasa ba mu san inda muka dosa ba, magabata kuma na ta gara mana tunani. Wannan ya ce kaza za ka yi ka yi nasara, wannan ya ce wancan... Har ka matashi ya rasa na kamawa, kullum a cikin zulumi da tunani.

Baba Bello Ado Hussaini kuma ya ce, "da boko ko sana'a, kawai mu ganka da rufin asiri, shi ne. Duk fafutukar neman rufin asiri ake". Mutanen yanzu kuwa sun fi girmama mai akwai (kuɗi), it doesn't matter a me ka tara, kasuwa ko ofis, a gona ko kwangila, kawai a gan ka da rufin asiri.

Engr. Ibrahim Babangida kuwa ya ce, "it doesn't matter, ilimi a ko'ina ne ka koya, a titi ko a makaranta, ya kasance ilimin ya maka sanadiyyar samun abinci, ka tsaya da ƙafafunka. Ana neman ilimi d abinci a ko'ina. Ilimi, ilimi ne.

Ka nemi duk abin da zai rufa maka asiri, ka sanya wadatar zuci, ka bar wa Ubangiji ﷻ sauran lamari. Wani arziƙinsa da ɗaukakarsa a gona ce, wani a kasuwa, wani a siyasa, wani a ofis... a yau mun ga wanda zagi ma yake yi ake ba shi miliyoyin ₦aira da dollars.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments