A cikin kuskure akwai darussa ga mai hankali. Kuskure shi ne aikata ba daidai, da zai haifar da sakamakon rashin daidai, sakamako maras kyau.
Kuskure, ko ba naka ba ne, ba kai ka aikata ba, kana da darasin ɗauka don gyara taka rayuwar. Kowa yana kuskure, kuskure ɗabi'a ce ta mutum.
Idan ka ji a ranka ma ka fi ƙarfi aikata kuskure, hakan ma kuskure ne da zai iya costing rayuwarka a yanzu ko a gaba. Ana iya yin kuskure a komai na rayuwa, zaɓi, alaƙa, ibada, furuci, tafiya... ana iya yi wa Ubangiji, iyaye, abokan alaƙa, iyayen gida kuskure. Babban abin da ke sanya ɗan Adam aikata kuskure shi ne, BIN SON ZUCIYARSA, ko JAHILCI, ɗan Adam ya zaɓi abin da yake so fiye da abin da yake buƙata, ko rashin gogewar rayuwa...
Babu rukunin mutanen da suka fi tafka kuskure a rayuwa da zai taɓa rayuwarsu ta gaba kamar matasa (18 - 35), a lokacin suka fara mallakar hankali, ƙarfin sha'awa, burace-burace... A lokacin matashi yake jin ya isa ma kansa zaɓin rayuwa, yake tunanin iyayensa da manynsa 'old school' ne, ba su san zamani ba (yana jin ya fi su wayewa), shi ma zai iya yi wa kansa tunani da zaɓin career, alaƙa, son bushasha...
Daga cikin manyan kusakuran matasa akwai rashin jin magana da shawarar manya (musamman iyaye), rashin kula da amfani da lokaci, rashin iya tattali na kuɗi da kadara, zaɓin soyayyar abin da ake so fiye da abin da ake buƙata, nawa da kasala, wasa da dama, dogon buri... Aikata kuskure ba laifi ba ne, yana nuna kai ma mutum ne da ya gwada yin wani abu. Babban kuskure shi ne ka maimaita kuskure da a baya ya sanya ka da-na-sani.
Ka koya daga kuskurenka!
Kuskure 'signals' ne na wani saƙo da darasi da duniya ke son koyar da kai. Matashi! A shekarunka 18 - 35, shekaru ne na koyon rayuwa, a lokacin ake gwagwarmayar saitawa da gina rayuwa, don raino sabbin zubin halittar ɗan Adam da su rayuwa a duniyar gobe. Kuskuren da kai ka aikata a jiya da yau, darasi ne ga rayuwarka da rayuwar 'yan baya.
✍🏻Aliyu M. Ahmad
17th Dhul-Qi'dah, 1445AH
25th May, 2024CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives #Kuskure
0 Comments