ƊAUKAR MATAKI 1 ZAI IYA CANJA MAKA RAYUWA HAR ABADA


Ka gama degree ko diploma, kuma ba ka da wani 'skill(s)' da kake neman taro da sisi, ka karanta wannan bayanin kafin Ubangiji ﷻ ya kawo maka wani abin yi na dindindin:

1. GRADUATE TRAINEE PROGRAM (GTP)

Ka san bankuna da kamfanoni sukan ɗaukar 'fresh graduates', suna koya musu aiki na tsawon watanni ko shekaru, kuma kana musu aiki suna biyan ka? A ƙarshe ma wasu su ba da 'permanent offer'. GTP kyakkyawar hanya ce ta 'capacity building' na 'career', kuma tafi kusa ga samin aiki a duk lokacin da aka zo ɗaukar permanent ma'aikata a wurin da kake GTP. Sau da yawa ma ba su sakin GTP beneficiary.

Idan a garinku akwai banki ko wani kamfani, ka kaɗe takardunka ka je ka ce kana son yin GTP, idan akwai dama za su yi maka bayani, ko kuma ka je Google ka yi searching 'Graduate Trainee Program' a Nijeriya, da yawan bankuna da kamfofi suna da wurin applying GTP a kan shafinsu.

Akwai wanda na sani da ya yi GTP a banki a Kaduna, daga baya suka ɗauke shi permanent, ₦220k - ₦250k suke biyansa (idan na riƙe), kuma su suka kama masa 'lodge', hatta 'transport' da motar banki suke tafiya da sauran 'staff'. Aikin banki ba shi da alaƙa da me ka karanta, matuƙar dai degree ce, kuma kana jin Turanci.

A pharmaceuatical industry, mai, kayan abinci, IT... duk suna bada damar GTP. Duba shafin Dangote, Shell, Nestle, MTN... idan ka shirya barin garinku (comfort zone).

2. AIKIN SA KAI (VOLUNTEERING)

• Kana da degree ko diploma kan 'education' kuma babu abin da kake yi sai jiran tsammani, yi ƙoƙarin neman wata 'secondary ko 'primary' mana a unguwarku su ba ka subject 1 ko 2 kana yi musu. Yawancin makarantu suna biya ma, ba zallar kyauta za ka yi ba.

Akwai makarantar da na sani, duk malamin da ya rage 'periods' aka ba wa ɗan 'volunteer' sai ya ba da wani abu idan aka yi musu salary. Abin da wasu masu volunteer ke haɗawa a wata, ya fi wanda wasu private schools ke biya, kuma babu takura da barazana kamar private schools.

Idan kuma kana sha'awar advanced academia, colleges, polytechnics da jami'a (university) suna bada damar 'volunteering'. Idan kana da kyakkyawan 2.1, kuma ka mastering field naka, kuma za ka iya lecturing ma ɗalibai, ka duba wata 'university' ta kusa da kai, ka nemi bayanin yadda tsarinsu yake, wasu makarantun suna biyan alawus. Idan ana neman ƙarin staff kuma sun san da zamanka.

• Idan kana da diploma a law, yi ƙoƙarin neman wata chamber ta babban barrister ka ce kana son koyon aiki, ko wata magistrate ko high court ka je volunteering. Za ka ƙara gogewa sosai, kuma duk sanda wata dama ta zo kana daga cikin waɗanda za su iya samu.

Akwai wanda ya yi 'diploma' a 'law', ya sami irin wannan shawara, ya je wata chamber yana koyon aiki, yana yi musu 'yan aike-aike. Sai da ya zo ya iya legal draft, rubuta agreements da sauransu. Wani lokacin barrister ya kan sa shi aiki, sai idan yazo ya karɓa ya gyaggyara, a ƙarshe ya nema masa admission LLB., ya ɗauki nauyinsa, shi ma ya zama barrister.

• Idan aikin jarida kake sha'awar yi, kuma ba ka samu aikin ba, garinku akwai gidajen radio, TV ko na jaridar takarda, rubuta letter ta neman yin volunteering, za ka samin 'hands-on experiences' a on-air programs, reporting skills, sound engineering... ya danganta da wurin da suka ba ka dama. 

Akwai kuma gidajen jarida (print media) suna bada GTP, ko volunteering. Akwai gidajen jarida na online, ka riƙa rubuta stories suna ɗora maka. Duk lokacin da aka sami 'fellowership' abin da suka fi buƙata shi ne rubutu, me ka taɓa rubutawa na report/story a matsayin ɗan jarida.

Akwai abokina da ya fara da volunteering, ya shafe kusan shekara yana zuwa gidan radio, a hankali yana koyon aiki, reporting, fassara... a ƙarshe ya zama 'staff', kuma yana rendering freelancing services na fassara. Yanzu haka yana kusan kammala master (self scholarship) sanadiyyar wancan mataki, juriya da haƙuri da ya ɗauka.

• Idan karatun lafiya ka yi, akwai damar volunteering a asibitoci, da samun dama kurkusa. Ka nema, dama suna neman ƙarin 'staff' ma'aikata sun yi ƙaranci. Part-time aiki ne, kuma su kan yi ihsani ma 'volunteers' da ɗan revenue da 'running cost' da suke samu. Ya fi zaman jiran tsammani.

• A aikin force na ɗan sanda da civil defense akwai 'special constabulary', wanda wasu daga baya suke koma permanent. Ka nemi bayanin ya ake shiga tsarin.

Volunterring yana da matuƙar amfani a 'portfolio' na CV naka. Domin zai nuna jajircewarka, sadaukar, son aiki da gogewa kan aiki.

3. KOYON SANA'A (SKILLS)

• Telanci - cikin sati 6 zuwa 10 idan ka maida hankali za ka iya koyon tako da yanka, musamman idan mai koya maka ba shi da aiyuka sosai kuma yana interest na ya koya maka.

• Business centre - idan akwai abokinka ko wani babban computer centre kusa da kai, ka nemi su ɗauke ka koyon aiki. Daga koyon aiki wani automatically za ka zama ma'aikaci a wurin, domin za a ce yi typesetting paper 1, yi wancan.. a hankali kana samun ₦500, ₦1k... kuma a hankali kana gogewa da 'hands-on skills', da yadda ake gudanar da kasuwancin business centre.

• Digital skills - data analysis, graphic design, social media management, affliate marketting... ka ɗauki 1 ka koya da gaske da naci. Wani skills yana buƙatar a ƙalla wata 3 ko fiye kafin ka gane ciki-da-bai, wani ma a cikin wata 1 za ka iya fara gane hanya.

Da 'digital skills' za ka iya freelancing a Upwork, Freelance, social networks (Facebook, WhatsApp...). Aiyuka da yawa ba sa buƙatar computer, wayar hannunka ta wadatar maka, kawai ka nemi ka koyi yadda ake yi. Idan kana 'content writing', kada ka damu da 'physical publication', akwai WikiHausa, Selar, Amazon Kindle... za ka iya ɗora littafinka ka saya da ebooks (PDF).

4. CONNECTION

Social skills, zumunci, girmama mutane, halartar taruka masu muhimmanci, abokai na gari, iya magana, aiyukan jinƙai da ƙungiyoyin sa kai... za su taimaka wa sosai a duk lokacin da wata dama ta zo a yi da kai.

5. GINA KYAKKYAWAN PORTFOLIO

Ka nemi yadda ake haɗa kyakkyawan 'curriculum viate' (CV) da resúme, ka yi amfani da social media wajen nuna me ka sani, me za ka iya. Ka gina social media profile naka da dukkan bayanan da suka shafi karatunka, check-in, aiyukanka, wurin da kake rayuwa...

Ka yi amfani da business/professional networks, irin LikendIn, Xing, Jobberman, NGCareers, Bizzybofy NG... ka yi amfani da portfolio sites domin nuna kwarewarka irin su Behance, GitHub, Carbonmade, Coroflot, Medium, Academia, UpWork, Freelancer, Fiverr...

Aiki sunansa aiki, da na ofis, da na gareji, da na kasuwa da shago... kowa ƙoƙarin kashe yunwar cikinsa yake. Rayuwa ba gaggawa ko gasa, kada ka zauna jiran tsammani kuma babu abin da kake taɓuka wa, kana zagin 'uncles' sun ƙi sama maka aiki. Wanda yake raba 'offer' wa mutane a 2000s, yau 'ya'yan cikinsa sun fi 5 suna jiran tsammani, ba yadda ya iya da su saboda yanayin. Bahushe ya ce, Allah ya ce tashi in taimake ka. Ka iya naka, ka yi addu'a, ka bar wa Ubangiji sauran.

✍🏻Aliyu M. Ahmad
9th Dhul-Qidah, 1445AH
18th May, 2024CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments