Wrong Bank Transfer


1. Idan ka yi 'wrong bank transfer', ma'ana, ka yi kuskuren turawa wata 'account number' kuɗi, wacce ba ita ka yi niyyar turawa ba.

Misali, 
Ka tura kuɗi ma 1234567890
Maimakon 1234567899 (ma'ana, an yi kuskure a lambar ƙarshe, an sa '0', maimakin '9').

Ko kuma,

2. Ka turawa wani/wata mai siyar da kaya a 'social media' kuɗi, amma ba su turo ma da kayan ba, kuma ka fahimci ba su da niyyar turo ma kayan (ma'ana dai, sun damfare ka).

Idan kana son dawo da kudinka cikin sauƙi (a sanina, yadda muke rubuta 'COURT ORDER'):

1. Za ka je 'Police Station' ko ofishin NSCDC (Civil Defence) ka shigar da ƙorafi, tare da bayar da bayanan afkuwar lamarin:

a. Sunanka da muhallin da kake zaune,
b. Rana da lokacin da ka yi transfer
c. Hanyar da aka yi transfer (ta P.O.S. ko 'mobile bank transfer').

* Idan 'mobile bank transfer' ne, za ka ba su bayanan asusunka (account details) da ka yi transfer da shi.

d. 'Account details' na wanda aka yi kuskure aka turawa kuɗi.
e. 'Account details' na wanda aka yi niyyar turawa kuɗi (sunansa, bankinsa da 'account number') asali.

Su kuma 'yan sanda (Police) ko 'yan Civil Defence' za su rubuta 'complaint letter' da bayanan da ka ba su zuwa ga 'kotu' ('Magistrate' ko 'High Court') don a yi ma 'COURT ORDER' ta maido da kuɗi.

2. Za ka tafi da 'letter of complaint' zuwa kotun da aka tura ka da takardar, su kuma za su rubuta ma 'COURT ORDER' mai ɗauke 'reference no.',  waɗancan bayanan (na sama), umarnin kotu na a maido ma da kuɗinka gareka, tare da sa hannun alƙali da hatimin kotu (court seal/stamp).

3. Za ka kai wannan 'COURT ORDER' zuwa ga banki (bankinka da ka yi transfer na kuɗi daga cikinsa), su kuma za su karɓi ƙorafinka tare da maido ma kuɗinka (amma fa wani yana ɗaukar kwanaki masu tsayi, musamma na 'inter-bank transfer').

ABIN LURA:

1. Kafin ka tura kuɗi ma wani ta waya (mobile bank transfer) ko ta P.O.S. yi ƙoƙarin tabbatar da 'bank details' da za ka turawa, shin babu kuskure? 'Acccount number' daidaice? 'Account name' daidai ne?

2. Idan ka bawa mai P.O.S. 'account number' ba daidai ba, ya tura kuɗi, babu yadda zai iya dawo ma da kuɗinka, har sai kun bi waɗancan matakai. Ko kuma shi ya shigar da ƙorafi ga bankin da yake yi wa 'agent'.

3. Za ka iya shigar da ƙorafi a matakin farko ta hanyar ƙiran 'customer care' na banki, idan kuma 'transaction' da ka yi na kasuwanci ne aka damfare ka, a shawarce; ka nemi lauya (legal practitioner).

✍️Aliyu M. Ahmad
11th Rabi'ul Thani, 1444AH
6th November, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #FasaharZamani

Post a Comment

0 Comments