Ka Zamewa 'Yar Uwarka Abokia


Idan kana da ƙanwa ‘mace’, 
Abokina!
Yi ƙoƙarin ka zame mata ‘aboki’.

Eh, aboki! Ka zama da kai ne take iya tattauna matsalolinta, damuwar ko neman shawararka. Idan kuma ka ɗan sami kuɗi, ka riƙa ba ta kyauta akai-akai, ba ma sai ta tambaya ba (don biyan ƙananan buƙatunta).

Yawanci idan ka ga yarinya ta yi abota da wani namiji a waje (‘bestie’), a cikin classmates, ko ‘ya’yan makwafta/unguwa, da yawa sun yi rashin samun kulawa ne daga gida, ba su sami wanda za suna faɗawa damuwarsu ya saurare su ba. A halitta kuma, mace ‘yar son kulawa ce, a duk inda tafi samu, nan take kai kanta.

Idan ba ka yi wa ‘yar uwata gata ba, na ƙananan ɗawainiyyarta (ka bar shi a hannun ‘saurayi’), kar ka yi mamaki don wani yana juya ta fiye da kai, kana mamaki ta yi masa hidima (kulawa, har girke-girke…) ko idan lokaci guda ka zo, kana son nuna mata iko, ta bijere ma.

Ba kuma wai da ƙarfi-ƙarfi, ko kuma faɗa mata za ka yi kai-tsaye ba, “KE NA ZAMA ABOKINKI, KINA FAƊA MIN DAMUWARKI”, a’a; mu’amalarku ta yau-da-gobe, ja-a-jika, kyautatawa, tausasawa, tattaunawar sirri… shi zai sa ta saki jikinta gareka, HAR KU YI SABO, har ta iya tattauna damuwarta da kai. 

✍️Aliyu M. Ahmad
10th Rabi’ul Thani, 1444AH
5th November, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments