MENE NE YA DACE DA KAI?

Ku zo mu yi duba na tsanaki:

• Misali na farko:

Wani zai ce, kada ka yi saving kuɗi kana ƙuntatawa kanka, ga buƙatu a tattare da kai. Kuma shawara ce mai kyau ta wata fuskar.

Amma idan ka yi duba na tsanaki mai wannan maganar AIKIN ALBASHI yake, duk wata yana da garanti jin alert na salary. Kai kuwa da aiki ne yake zuwa yau, gobe babu, ko kasuwa ce yau da ciniki gobe babu, ko kayan da kake siyarwa seasonal ne.

Shin shawarar nan tasa ta dace da kai?

• Misali na biyu:

Wani zai ce maka, idan ka sami ₦10 million, kada ka gina gida, ka kama haya; kuɗin sai ka riƙa juyawa, daga ribar sai ka gina gida.

Ita ma wannan shawara ce mai kyau ta wata fuskar.

Amma idan ka duba mai bada wannan shawarar a Kano, Kaduna ko Bauchi yake zaune, wuraren da zama gidan haya normal ne, ba aibu ne.

Kai kuwa da a garinku kamar Haɗejia ne, zama gidan haya aibu ne. Wataƙila gidan su budurwarka aka ji gidan haya za ku zauna za a fasa ba ka aure.

Shin waccar shawarar ta dace da kai?

• Misali na uku:

Wani zai ce, idan ba science courses ba, zuwa jami'a ka ɓata shekaru 4 ɓata lokaci ne. Ba yadda za a yi ka yi karatu ka dawo ba aiki.

Ita ma wannan shawara ce mai kyau ta wata fuskar.

Amma idan ka yi duba, mai wannan maganar ya samu scholarship a gida, kai kuma karatun diploma ko NCE kai ka ɗauki ɗawainiyyar kanka a daddafe, kuma kana da sana'a ta rufin asiri da idan ka yi nesa da gida, mkarantar ma ba lalle ka iya ba. 

Shin maganarsa ta dace kai?

• Misali na huɗu:

Kada wani ya ruɗe da aikin albashi ko kasuwanci; babu hanya ɗaya da aka ce dole kan ta za a yi arziƙi. Kowacce harka ta rayuwa akwai ƊANGOTENTA, akwai KAMAYE, ka riƙe abin da ya zo maka da kyau, za a iya excelling. 

Mu fahimta:

A lokuta da yawa, ka fara duba mai magana kafin maganar, saboda wasu suna yi wa rayuwa hukunci ne da yanayin da suke ciki. Social media kuma ta haɗa mutane daban-daban, a shekaru, jinsi, muhalli wajen zama, iyaye da tarbiyyar, tattalin arziƙi, zurfin ilimi da tunani... ka riƙa tsintar me ya dace da kai, mene ne ba naka ba, kada kuma ka bari 'information overload' ya hana ka sukuni.

✍️ Aliyu M. Ahmad
27th Satumba, 2025

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments