Abinci: Kar Mu Ɗauka da Wasa!


Muhimmiyyar shawara da zan bayar a yau, ita ce; idan kana da hali, kuma kana da iyali, ka yi ƙoƙarin sayan kayan abinci ka adana, wannan na daga cikin 'fiqhun' Annabi Yusuf عليه السلام, na fassarar mafarkin 'Aziz' (Yusuf, aya ta 43 - 56).

Da dukkan alamu, da kuma hasashen masana (FAO), akwai yiwuwar samun ƙarancin abinci saboda ambaliyyar ruwa ta shafe amfanin gonaki, ga yaƙin Russia da Ukraine, ƙaranci noma a yankunan da ƴan bindiga suka mamaye, gashi kuma an garƙame iyakokin ƙasar (ba za shigo da abinci daga waje ba), farashin kayan abinci na ƙara tashi, ga rahotanni da ake samu, masu hannu-da-shuni na bin 'karkara' da 'kasuwanni' suna ta wawashe kayan abinci suna adanawa.

Duk matsin da za a shiga, matuƙar gidanka aka fi ƙarfin yunwar ciki, tom da ɗan sauƙi, sauran abubuwa kuma da dole ba sai a haƙura da su.

Matuƙar akwai yunwa, dole a sami rashin tsaro. Yunwa ba abin da ta bari, dole sai an ci, za a rayuwa, a yi ibada, a yi harkokin rayuwa. Hatta imani mai lago-lago, yunwa illata shi take. Sai kuma a dage da addu'a da istighfari, mu gyara halayyenmu, mu koma ga Allah, mu yi ƙoƙarin zaɓen shugabanni masu kishi da son kawo sassauci.

✍️Aliyu M. Ahmad
12th Rabi'ul Thani, 1444AH
7th November, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #FoodCrisis

Post a Comment

0 Comments