A Wajen Rubuta Sunan Allah ﷻ

Sunan 'Allah' keɓantaccen suna (proper noun) ne.

1. A ƙa'ida ana rubuta harafin farko na keɓantaccen suna (proper noun) da babban baƙi (capital letter) [Huddleston et al, 2002].

Ya saɓawa ƙa'idar rubutu (othorgraphy/قواعد الاملاء) rubuta 'proper noun' da ƙananan baƙi. Misali, harafin farko (a) a sunan "Allah", da babban baƙi ake rubuta ta a kowanne muhallin jumla (farko, tsakiya ko ƙarshe):

• (A)llah ✅ 
• 'allah' ba ❌

2. Girmamawa ne rubuta sunan Allah ko lamirinSa (pronoun) da babban baƙi (reverential capitalization).

Ma'ana, a wajen rubuta katsattsen lamirin (personal pronoun), ko na mallaka (possessive)... ko 'zagin aikatau', siffofi (adjectives) da suka danganci Ubangiji, ana fara rubuta su da babban baƙi. Misali:

-------------------------------------------------

• KATSATTASEN LAMIRI (PERSONAL PRONOUNS)

"Godiya ta tattaba a gare (S)hi"
[Rum, aya ta 18].

NB: 
Kalmar 'shi' tana farawa da babban baƙi.

-------------------------------------------------

• LAMIRIN MALLAKA (POSSESSIVE PRONOUNS)

"...da mala'ikun(S)a, da manzannin(S)a, da littafan(S)a..."
[Baqara aya ta 285].  

NB: In mun lura, kalmar mallaka (sa) tana farawa da babban baƙi, saboda nunin mallaki ne ga Ubangiji (Allah).

-------------------------------------------------

• SIFFA (ADJECTIVES)

Misali:

1. "Allah (M)asani ne ga abin da ke cikin ƙiraza."
[Ali-Imran, aya ta 153]. 

NB: Kalmar 'masani' ta fara da babban baƙi, saboda a nan, siffar Allah ce.

2. "Da sunan Allah Mai rahama, Mai jin ƙai"
[Fatiha, aya ta 1].

Kalmar 'mai' tana farawa da babban baƙi, amma wacce take biyo bayanta (rahama, jin ƙai...), za a barta da ƙananan baki. 

Sauran misalai, 
• Mai ji, 
• Mai gani,
• Mai basira, 
• Mai.... dss.

-------------------------------------------------

• ZAGIN AIKATAU

"Allah (Y)ana halitta abin da (Y)ake so"
[An-Nur, aya ta 45]

Kalmomin 'yana' da 'yake' suna nuni da aiki, sun fara da babban baƙi na 'Y' saboda nuni da keɓewa da kuma girmamawa gare Shi (Allah).

وصلى الله على نبينا وحبيبنا محمد ﷺ وعلى أزواجه وذريته وصحبه وسلم.
✍️ Aliyu M. Ahmad 
10th Dhul-Qaadah, 1443AH
10th June, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliyuTheLinguist 
Photo Credit: The Humblei

Post a Comment

0 Comments