A Ba Wa 'Ya'ya Tarbiyya Daidai da Zamani


Ba ga iya ƴaƴa MATA ba, har da ƴaƴa MAZA ma

Ta hanyar amfani da 'apps', ko karɓar wayar kai tsaye; ina goyon bayan iyaye da su riƙa bibiyar wayoyin 'ya'yansu akai-akai, domin ganewa idonsu da kuma kula da kiwon da Allah Ya ba su na tarbiyya (At-Tahrim, aya ta 6):

👉 Me ƴaƴan suke aikatawa da wayoyin hannunsu? Alheri ko sharri.

👉 Da waɗanne kalar mutane suke mu'amala ta cikin wayoyinsu?

• Za ka gama ba wa yarinya tarbiyya tsaf, wani da wayar hannu zai ruguza mata tarbiyyar da ka yi shekaru kana ginawa. Ko kuma, yaronka na da tarbiyya a zahiri, amma sheɗani ne a cikin waya, yana lalata ƴan mutane. 

• Ga yaudara, da soyayyar ƙarya, a zahiri ka hana ƴarka tsayuwa da samari a ƙofar gida, amma ta cikin waya tana 'dating' samari kala-kala, wataƙila ciki har da abokinka 'baba' (yana cin amanarka), ko wani ɗan uwanta na kusa na kunya, tana kula wanda ta sani, da wanda ba ta sani ba, wanda ya kamata, da wanda bai kamata ba, duk ta cikin waya.

👉 Duba waɗanne shafuka suke ziyarta. Kamar a duniyar zahiri, akwai wuraren alheri, akwai na banza. Akwai mutanen kirki, akwai na banza. Akwai 'contents' masu amfanarwa, akwai masu halakarwa a tunani ko lalata tarbiyya.

👉 Waɗanne irin videos suke kalla, waɗanne irin sautuka suke sauraro. Yawancin waƙoƙin 'hiphop', daga batsa sai shirka, sauraron sauti ba iya daɗin amon murya da kiɗi ba ne, yana da tasiri ga ruhi, haka 'films' na da tasiri ga tunani.

👉 Duba yanayin lokutan da yara ke ɓatawa da wayoyin hannunsu. Wayar hannu tana kashe kwazon mutane da dama, musamman a makarantu, ko wajen aiki; maimakon a maida hankali wajen karatu ko aiki, sai a shashance da danne-danne waya kan abubuwan marasa muhimmanci, har abin ya zama jaraba (addiction). 

Media ta zamewa duki wani ɗan da yake rayuwa a ƙarni na 21 sashen rayuwa. Muna wani zamani ne, da hana yara amfani da waya abu ne mai wahala, kasancewar duk kusan abubuwan da suka shafi al'amuran yau da kullum: karatu, kasuwanci, harka da banki sai da 'smart phone' ko 'internet'. 

Imam Ali رضي الله عنه ya yi wata nasiha mai tsada tun wancan lokacin, yake cewa: "IYAYE! KADA KU RAINI ƳAƳANKU KAMAR YADDA IYAYENKU SUKA RAINE KU, DOMIN AN HALICCE SU A WANI ZAMANI BA IRIN NAKU BA" (Ighathat Al-Lahfan 2/265). A ba wa ƴaƴa tarbiyya daidai da zamani.

Duk canjawa da juyin zamani, Shari'ar Musulunci, ba abin da ya canja, na haramci da halacci, a kowanne hali, a zahiri, ko a media, misali: kallo batsa, ko bibiyar shafukan taɓararru, mujahara (bayyana laifi), misali, rawar 'yan mata, tabarruj (ɗora hoto da matsattsun kaya, ba lulluɓi) fitana ne, yaɗa labaran ƙarya (fake news), gulma, annamimanci, ƙazafi, rashin kunya wa manya ko cin zarafin mata, jin daɗin hira da ajnabiyya, ha'inci da zamba (fraud), yaɗa ɓarna... DUK FITINA NE, HARAMUN NE.

✍️Aliyu M. Ahmad
23rd Rabi'ul Thani, 1444AH
18th November, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments