Ka Riƙa Ɓoye Damuwarka


Ka ɓoye damuwarka, don ba kowa ne ne zai damu da damuwarka ba. Babu wanda ba shi da wata damuwa, sai dai wanda ya fi ka daurewa da ɓoyewa.

Ko ga waɗanda ka shiga damuwa ta dalilinsu (masoyanka), rauni (weakness) ne ka bayyana musu ka shiga damuwa, nuna damuwa ga wanda bai damu da damuwarka ba, tamkar ba shi makamin yaƙarka ne. Wasu kuma tamkar ka ba su labarin hirarka a bayan idonka ne.

Ka koyi ɓoye damuwarka, MATUƘAR BA TA NEMAN AGAJI BA CE. Waɗanda suke masoyanka na haƙiƙa, idan sun ji labarin kana cikin damuwa, jin hakan zai sanya su cikin damuwa, saboda masoyinsu na cikin damuwa.

Su kuma maƙiyanka masu adawa da kai za su yi farin ciki da jin daɗin kana cikin damuwa (kenan ka cutar da masoyanka, ka farantawa maƙiyanka kenan).

Lokacin da ka mutu ne kaɗai, kowa da kowa zai nuna ya damu kai, musamman zamanin 'media', a 'status', 'stories' da 'timeline', ana nuna damuwar rashinka. Ana bayyanawa ɗan Adam damuwa ne, idan zai iya bayar da agaji don a fita daga cikin damuwar. Duk damuwar da ta fi ƙarfinka, maganinta Allah, ka maida lamarinka gare shi, ka taƙaita ƙorafi ga raunana (mutane).

#AliyuMAhmad
#AliMotives 
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments