Komawa Makaranta

 


Wasu abubuwa da za (iya) su faruwa bayan an koma makaranta, daga dogon yajin aiki:


1. Rikici da masu gidan haya.
Gaskiyar magana idan ka san 'tenancy' na shekara ka biya (mis. November, 2021 - November, 2022); kuma lokaci ya cika, duk da ba ka zauna a ciki ba, sai ka sabunta (sake biya). Kar ka yi rikici da 'landlord', sai dai ka nemi alfarma, ya sautata ma.

Idan kuma yarjejjeniyarku ta haya, ta 'session' ce, kamar yadda wasu ke yi, sai an ƙarasa 'session', tukun hayarka ta ƙare.

2. Kar ka damu don a tsawon lokacin yajin aiki, wasu daga cikin abokanka ba sa ma zumunci. A rayuwa, dole ne sai ka yi mu'amala da wasu, wani dalili zai haɗa ku; abokai kuma kala-kala ne.

Akwai waɗanda suke tamkar ganyen bishiyi, akwai rassa, akwai kuma jijiyoyi. Akwai mutanen da za su shigo rayuwarka na ɗan lokaci sanadiyyar wani dalili (admission), da zarar dalilin ya kau (bayan graduation), za su shuɗe, sune HAƊUWAR GATE, RABUWAR GATE.

Akwai mutane da dalili ne ya haɗa ku, amma rashinsu a rayuwarka zai ƙuntata ma, akwai iyayen gida, malamai... (waɗannan tamkar rassa suke). Akwai kuma abokai na dindindin, duk matsayin da in ka taka a rayuwa, kuna tare, yawancinsu; abokanka ne na yarinta ne (waɗannan sune tushe/jijiya).

Yawancin abokan karatu (schoolmates/course mates/roommates), musamman na jami'a, an haɗu ne dalilin karatu, idan an tafi hutu, dalili ya yanke (abota ta tsaya); idan an dawo (resumption), sai a ɗora a inda aka tsaya (haka abin yake, ba wani abu ba ne na damuwa).

3. Ɗakin hostel/lodge ɗinka na buƙatar gyara na musamman. Tsawon lokacin da aka ɗauka, ya yi ƙura sosai (musamman da damina ta gifta), akwai ɓuƙatar ka koma kwana ɗaya kafin fara karatu.

4. Ba za ka koma tare da wasu abokan ba; wasunsu sun mutu, wasu sun sauya makaranta, wasu sun ajiye karatun ma saboda yanayin rayuwa.

5. Farashin kayan abin ci ya sauya sosai, daga February zuwa yau (October).

Ga tsada, kuma babu kuɗi a hannun mutane sosai, kar ka takurawa kanka, ko mahaifinka ko wani mai ɗaukar nauyinka. Rayuwar da aka yi watanni 8 baya, ta sauya da ta yau sosai.

Misali, a yanzu:

• Cooking Gas 1kg = ₦850+
• Noodle (120g) = ₦5,500+
• Spaghetti 1 Cartoon (20pcs) = ₦6,500+
• Shinkafa (1 mud) = ₦1,400+
• Cooking oil (OK) = ₦1k+ (Groundnut oil) = ₦1,200+
• Photocopy (1 paper) = ₦20

Akwai sauran spices, kayan shayi, man shafawa, sabulun wanka da wanki, material na karatu... hatta kuɗin motar haya (transport) ya sauya. Akwai buƙatar fara tanadi, tun yanzu.

6. Za a gajarta zangon karatu, shashanci ba na ka ba ne, ka fara shirin maida hankali ga karatu, wasu hidindimun da ba dole ba, sai an jingine su. Karatu lokaci ne, in ya wuce, shikenan!

-------------------------------------------------------------------------
*Zan ɗora "English Version" a #DigitalNASELS
-------------------------------------------------------------------------

✍️Aliyu M. Ahmad
16th Rabi'ul Awwal, 1444AH
12th October, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments