Wankan Juma'a

Wankan Juma'a sunnah ce mai ƙarfi, saboda Manzon Allah ﷺ Ya umarci Musulmai da cewa, duk wanda zai je sallar Juma'ah, to ya yi wanka (Bukhari, 882).

Ana yin wankan Juma'a kamar yadda ake wankan 'janaba'. Za a yi niyya, a yi 'bismillah', sai a fara da alola (amma za a wanke gaɓɓai alola sau ɗai-ɗai), ban da ƙafa (ita sai a ƙarshe). Sai a wanke kai zuwa wuya sau 3 (a cuccuɗa sosai), sai a wanke tsagin jiki, na dama sau 3; daga kafaɗa zuwa singalin sawu (ban da ƙafa), a zuba ruwa ana cuccuɗawa, sai kuma a dawo tsagin hagu (shi ma haka), sai kuma a wanke ƙafafu (daga ƙarshe). 

Idan kuma akwai 'swimming pool' ko 'kogi', za ka iya yin niyya, ka faɗa, jikinka ya jiƙa da ruwa (wannan ma ya wadatar). Ana iya (yin) wankan Juma'a tun daga fitowar 'alfijir' na ranar Juma'a har izuwa lokacin tafiya masallaci, amma yin wankan a lokacin da ka zo tafiya masallaci shi ya fi (ka sada shi da sallah). Za ka iya farawa da wankan 'sabulu' (tabarrud), sannan sai ka yi na Juma'ah a ƙarshe (saboda shi kamar alola ne).

Sauran sunnonin/laduban Juma'a sune: tsaftace baki (da 'aswaki' ko 'brush'), yanke farce, sanya sutura mai kyau da turare mai kamshi, tafiya masallaci da wuri (kafin hawan liman mumbari domin sauraron khuɗuba), yawaita adhkar da Salatin Annabi ﷺ, da yin addu'o'in alheri.

Za ka iya karanta Suratul Kahf tun daga faɗuwar ranar Alhamis, zuwa faɗuwar ranar Juma'a (Faydul Qadir, 6/199). Haramun ne yin magana/surutu/'chatting', shagala (mis. danne-dannen wayar hannu), ko cinikayya/kasuwanci a lokacin da liman ke khuɗuba (Al-Juma'a, aya ta 9). 

Sallar Juma'a tana sauƙa a kan matafiya da mai jinya mai tsanani, amma duk mazaunin gidan da ya tsallake Juma'a 3 a jere, da gangan, Ubangiji zai rufe zuciyarsa (Abu Dawud, 1052).

Allah Ya amsa mana ibadu 🤲

✍️Aliyu M. Ahmad
25th Rabi’ul Awwal, 1444AH
21st October, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari  #MusulunciDaRayuwa #Jumaa

Post a Comment

0 Comments