Tsoron Mage (Ailurophobia)


Mutumi da yake da wannan matsalar ‘ailurophobia’, shi ne, wanda da zarar ya ga kyanwa/mage, zai ‘tsorata’, bugun zuciyarsa zai ƙaru, wasu har da ihun tsoro, kuka, ko shiɗewa/rikicewa, wasu har ‘suma’ suke idan ta hau kansu.

Abin da ke kawo wannan matsalar, wasu tun daga yarinta ne, idan ana tsora ta su da ‘mage’. Wasu iyayen ko masu raino a wajen bayar da tarbiyya, suna kuskure, suna maida ‘ya’yansu ‘lusarai’, ta hanyar tsoratar da su lokacin suna ƙananan yara da abin tsoro, kamar ‘mage’, ‘ɓera’, ‘dodo’, da sauransu; sai su tashi da tsoron ‘abin’.

----------------------------------------------------------
Misali, yarinya, ‘yar shekara 3/4, Siyama da ta rasu a 29th September 2022, sanadiyyar fyd* da wani mutum ya yi mata, ta hanyar tsoratar da ita da ‘mage’. A rahoton da Bilya Abubakar Muhammad na ranar 2nd October, 2022 da na ‘Daily Trust’ na 8th October, 2022; lokacin da Siyama ta haɗa ido da shi (mutumin) a CID, kuka ta fara tana cewa: “Umma ya ce kashe ni zai yi da almakashi, me ya sa kika faɗawa Abba? Kashe ni zai yi, kuma ya haɗa ni da MAGE”, daga nan zazzaɓi ya kamata, washegari ta rasu/mutu.  
----------------------------------------------------------

An ce Adolf Hitler (1889 - 1945), Alexander the Great (356 – 323BC), Mussolini Benito (1883 - 1945) da Napoleon Bonaparte (1769 - 1821), Julius Caeser (100 – 44BC) na daga cikin manyan mutunen da suka sha fama da ‘ailurophobia’ a tsawon rayuwarsu. SUN BA WA MAZA TSORO, MAGE TA BA SU TSORO.

Ibn Ƙayyim Al-Jawziyya (691 – 751AH) cikin Tuhfah al-Maudud, shafi na 158, “Ya kamata a nisantar da yaro daga dukkan wani sauti ko wani abin kallo mai firgitarwa da tsoratarwa, domin (rashin nesatarwa) na iya cutar da ƙwaƙwalwarsa tun yana ƙarami”.

An ruwaita daga Ibn Abi Layla (17 - 83AH) cewa; Manzon Allah ﷺ na cewa: “baya halarta ga Musulmi ya tsoratar da Musulmi” (Abi Dawud 5004).

Ana magance matsalar tsoron mage (ailurophobia), da sauran halittu ta hanyar ‘cognitiɓe behaɓioral therapy (CBT)’, ma’ana, ta hanyar tattauna da kwararru, don su canjawa mutum wancan tsoron cikin tunaninsa. Ko ta hanyar ‘exposure therapy’ na Joseph Wolpe (1915 – 1997), kwararre zai canjawa mai ‘ailurophobia’ tunani, ta hanyar nuna hoton mage, zuwa hoto mai motsi, har a kai ga 'toy' na mage, zuwa taɓa mage ta zahiri. 

✍️Aliyu M. Ahmad
23rd Rabi’ul Awwal, 1444AH
19th October, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari  #Psychology #Ailurophobia #Phobia

Post a Comment

0 Comments