Harshe ko Yare


Harshe shi ne yaren da ake yake da masu magana da shi da yawa, ciki da wajen muhallin masu yaren na asali (native speakers), kuma ana amfani da wajen binciken ilimi, da sabbabin kafafen yaɗa labarai na zamani. Misali, harsunan Hausa, Yoruba, Igbo, Turanci, Larabci, Faransanci, dss.

Yare kuma, shi ne yaren da ake amfani da shi a iya muhalli masu magana da shi na asali (native speakers), ba za ka same shi a wajen muhalli ko kafafen yaɗa labarai, ko ana amfani da shi wajen binciken ilimi ba. Misali, Ishekiri, Urhobo, Idoma, Igala, da sauransu.

Misali:
✅ Harshen Hausa, Turanci, Larabci...
❌ Yaren Hausa, Turanci, Larabci....

A wajen masana nazartar harshe, kuskure ne ka ƙira Turanci, Larabci, Hausa, Sinnanci... da YARE, sai dai HARSHE, domin ƙiran su da 'YARE' rage musu matsayi ne. Ko a nazarce, ana cewa, ilimin harshe (lingustics/لسانيات), ba 'ilimin yare ba'.

Na samu wannan ilimin da maigidana a rubuce-rubucen adabi, 'Chairman' na Ƙungiyar Marubutan Jihar Jigawa, Mallam Hasheem Abdallah .

✍️Aliyu M. Ahmad
28th Rabi'ul Awwal, 1444AH
24th October, 2022CE

#AliyuMAhmad #Linguistics

Post a Comment

0 Comments