Mu Kula


Aiki ne mai wahala, ko a wajen malaman halayya (psychology), cewa; sai ka (tursasa wa kanka) ƙoƙarin fahimtar/bin diddigin (abin da ya ɓoye daga) halayyar mutane, mis. miji/mata, masoya, abokai, abokan zama...(Wilson, 1998). Kai dai ka mu'amalanci kowa da abin da ya bayyana ma (na alherinsu), kar ka bi diddigin abin da ya ɓoye... sai dai ma ka sa kanka cikin damuwa (PTSD).

Kar kuma ka ce za kana fassara mutane da irin abin da kake gani yau-da-gobe a 'internet,/social media', na 'quotes', ko wasu 'littafan halayya' ko 'rubuce-rubuce', labarin rayuwar mutane daban-daban ne, haka tunaninsu, muhallinsu, yanayin da ka tsince su...

Misali, wani ya rubuta ALAMOMIN DA KE NUNA MIJINKI NA ƘAUNARKI DA GASKE, sai ki duba ki ga (mijinki) ya gaza da wasu (daga cikin waɗanda aka lissafa), ki sa wa kanki damuwa, da tunanin, shin ko da gasken (mijinkin) yana ƙaunarki? Ko abokan zamanku/masoyanku sun gaji da ku, ku ɗauka kuna ƙoƙarin fassara su da abin da wani ya rubuta a 'social media', kuna sa wa kanku damuwa.

Wani mai hikima na cewa: "لن تندم أبدًا على كونك طيبًا، عامل الناس بأخلاقك لا بأخلاقهم، لن تندم أبدًا على كونك طيبًا، إذا أردت أن لا تندم على شيء، افعل كل شيء لوجه الله" ma'ana: "ka mu'amalanci mutane da ɗabi'unka (kyawawa), ba da irin nasu ɗabi'unsu ba; ba za ka taɓa nadamar kyautatawa mutane ba. Idan ba ka son yin nadama, ka yi komai domin neman yardar Allah".

✍️Aliyu M. Ahmad
1st Rabi'ul Thani, 1444AH
27th October, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives #Psychology

Post a Comment

0 Comments