Canjin Kuɗi


Canji Kuɗi

Duk wannan rubutun 'Ajamin' shi ya tsole musu ido, an yi nasarar cirewa a ₦5, ₦10, ₦20, ₦50 da ₦100; shi ya sa yanzu ka ji an ce, canjin daga kan ₦200, ₦500 da ₦1,000, sune 'notes' da suka rage, masu rubutun 'Ajami'. 

Yanzu sauran "نصر من الله" ta jikin bajon sojoji kuma. Kafin a yi riginar IOC, mu yi ta zama babu kishi, sai yadda suka so.

Kafin zuwan Turawa Arewa a 1903, yankin Hausawa, Musulmai, da 'script' na 'Larabci' suke amfani wajen rubuce-rubuce don isar da saƙo, wannan dalili ya sa aka rubuta 'Ajamy' a jikin ₦aira.

Larabci harshe ne, eh! Kuma shi ne 'official language' na addinin Musulunci; amma ba shi ke nuna Musulunci ba, don akwai Larabawa da ba Musulmai ba. Larabci harshen 'Saamiyya' ne da danginsu ɗaya (a language family) da Yahudanci (Hebrew), Somali, Hausa, Kanuri Buzanci da Habashanci. Asalin harafan Larabci daga 'hierogylph' ne na 'Nabataean', ba wai Musulunci ba. Harshe don isar da sako ne, a jikin kuɗi, ba don addini ba.

✍️Aliyu M. Ahmad
30th Rabi'ul Awwal, 1444AH
26th October, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments