Masoya: A Karba Da Hakuri


Ban sani ba, ko akwai wanda (wannan shawarar) za ta amfana 👇👇

Daga shawarwarin zamantakewa da na taɓa bayarwa, ban taɓa jin wacce na bayar, kuma na gamsu da ita ba, kusan 100%, kamar wannan:

Ya ce min, wai ya sha rutsa budurwar da zai aura, tana kula tsofin samarinta (exes), har ma da wasu ƙarin samari, a gida, da social media, shi kuma abin yana matuƙar damunsa sosai, kuma idan ma yana nuna (mata) ɓacin rai, a ƙarshe, sai ya zo, shi yake bayar da haƙuri, da lallami... don yana son ta sosai.

Wannan yi masa kishiyoyi (yana ɗaukarsa a matsayin cin amanar) don yana matuƙar kona masa rai, duk da bai gaza yi mata kowacce irin hidima da saurayi ke yi wa budurwa ba (daidai gwargwado), amma ba ta daina ba wa wasu 'attention' ba; a yanzu, ji yake ma kamar ya janye, ya haƙura, ko zai samu salama.

Ya samu mahaifiyyarsa kan damuwarsa, da ƙudurinsa, ta ce, ya je ya sake shawara, haka ma wakilinsa (kawunsa) ya ce masa".

Na ce ya ban lokaci na yi tunani. Bayan kwana 3, ni har ma na manta, ya ƙira ni, ya ce, ya ji shiru; na ce afwan, ya ƙira ni da daddare mu yi magana a waya.

Abin da na ce masa shi ne, kawai, YA YI HAƘURI, YA RIƘE BUDURWARSA, tunda har ta amince shi za ta aura. Dalili kuwa shi ne, idan ya ce zai rabu da ita saboda kula wasu samari, na farko; ita wannan (budurwar), a yanzu ya san halinta, tun har ana (iya)) samun saɓani, a daidaita.

Na biyu, BARIN BUDURWAR FARKO, KA NEMI WATA, ZAI IYA KASANCEWA, KAMAR MATUƘIN KWALELE NE DAGA KOGI, ZAI KOMA ZUWA TEKU; wacce zai je ya sake nema daga baya, bai san halinta ba, sai fa ya yi sabon aiki, GINA SOYAYYA DA YARDA, wataƙila ma ta fi ta farko iya kisisina...

Na ce, ba wai in a goyon bayanta ba ne, duk da abin da take (ita budurwar), a addinance, HARAMUN NE ta bawa wasu damar kulata (alhalin an yi 'khitba', tana da yaƙinin ita zai aura), idan ba ta ba su dama ba, ba mai kula ta, domin hakan haɗa fitina ne, yaudara ce, yana sa mutum tara siffofin munafukai (ƙarya (koda a da ba ta yi, za ta fara yi), da karya alkawari, da cin amana, da ɓoye-ɓoye).

Na ce, amma a yanzu ya yi haƙuri a hakan, har ta kai su ga ɗaura aure. Na ce, mace, ba a mata ƙarfafa, don sai ta nuna ma 'capacity', idan kana son horar da ita, bulala ɗaya ce; na ji wani dattijo na cewa, "sai dai ka hora da 'yar uwarta mace (kishiya)..."

Washegari, ya faɗawa wakilinsa ga shawarar da na ba shi, kawunsa ya ƙira ni a waya, ya tambayen, "na taɓa aure", na ce a'a, "shekarun nawa?" Na faɗa masa; ina soyayya ko an min baiko?... "amma kai kam Allah Ya ma baiwar zurfin tunani..., don ko ni, ban shawarar da zan bayar ba, da yanzu, maganar auren can ta tashi, an fasa..." Ya min godiya, da addu'o'in alheri.

Bayan sun yi aure, kamar da shekara 2, har matar ta haihu; sai ya tsiro da hidimar, yana son ya ƙara aure, hankalinta ya tashi sosai, har ta wani ɗan rame (a yadda yake ban labari). Amma fa a niyarsa, ba auren zai ƙara ba, wai, kawai ramkon wahalar da ta ba shi ne, kafin su yi aure, don ita ma, ta ji irin yadda ya ji... (amma ban ce a ɗauki mataki na biyu ba, na bayan an yi aure, a dai ci gaba da zama da haƙuri)

✍️Aliyu M. Ahmad
4th Rabi'ul Thani, 1444AH
30th October, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives #PhiloTherapy

Post a Comment

0 Comments