Addu'a


Tab! Yanzu sai a samu mutumin da zai iya yin wata guda cur, ko fiye, ba ya 'awrad', ba kuma ya ɗaga hannunsa sama, ko sanya goshinsa a ƙasa ba, ya roƙi Ubangiji wata buƙata (ma'ana, ba ya yin addu'a ta roƙo)? Ba kuma wai don ba shi da buƙatar komai ba ne, ko kuma ya wadata da komai da komai ba.

Idan ka kasance cikin waɗanda ba sa yin addu'a (ta roƙo) sai suna cikin matsi ko matsala, to fa tabbas kana cikin babbar matsala tsundum (a yanzu). Wai wani kunya yake ji ya ɗaga hannu yana addu'a, gani yake kamar za a fassara shi da wanda yake cikin matsala, ai kuwa kana cikin matsala tsundum!

Addu'a ibada ce! Kuma Ubangiji ﷻ Ya na fushi da mutumin da ba ya roƙarsa (ba kamar 'mutane' ba). Ka ɗaga hannu, ka roƙi Ubangiji duk buƙatunka ko neman albarka da neman kariya daga sharri, ko roƙan ma ƙasarmu zaman lafiya, ko roƙan ma waninka buƙata, kariya, lafiya ko nasara a rayuwa.

Ka kasance cikin tsarki (alola), ka fara da yabon Ubangiji ﷻ da salati ga Shugaba ﷺ, kana maimaita buƙatarka cikin ƙanƙan da kai tare da tawassali da siffofi ko halayyen Ubangiji ﷻ; a tsakiyar dare, ko bayan ƙiran sallah, ko a la'asariyyar Juma'a, ko bayan kammala alola, ko a cikin sujjada ko tahiya ƙarshen sallah, ko cikin halin tafiya (bulaguro), ko a lokacin buɗa bakin azumi (na nafila ko farillah), ko bayan kammala wani aikin alheri (mis. karatun Alƙur'ani Mai girma, zikiri ko sallah)...

Kai kodayaushe ne ma, ko yanzu-yanzu, ɗaga hannu ka roƙi Ubangiji buƙata. Matsala ce, a ce kana zama, ba ka addu'a!

✍️ Aliyu M. Ahmad 
8th Rabi'ul Awwal, 1444AH
3rd November, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments