Ba A Makara Da Neman Ilimi


Ba a makara a nema ilimi, 
Sannan ba a gaggawa a neman ilimi. 
Makararre shi ne wanda bai fara ba, ko da yaro ne.

Na taɓa jin labarin wani malami (na manta sunansa) a ƙasar Hausa, wata rana yana yawo cikin gari tare da almajirinsa, sai suka wuce ta wata makaranta, wani dattijo yana ta ƙoƙarin koyon Alƙur’ani da kyar, sai wannan Almajirin ya ce: “uhm! Wannan ai ya makara”. Malaminsa ya ce, “a’a, bai makara ba, mu yi gaba zan nuna ma makararre”. Suna tafiya, sai suka zo wani taro, ana ta kiɗa, wani dattijo yana ta tiƙar rawa, sai malamin ya ce: “to, ka ga wannan, shi ne ya makara.” 

Akwai mutane da yawa da shekarunsu suka yi nisa, waɗanda ba su sami damar zuwa makaratun ‘koyon addini’ ba, a yarinta; sai yanzu da girma ya kama su ne, suke tunanin ya za a yi, su koma ɗaukar karatu.

Wasu suna gani, sun girmi zuwa makaranta, ko kar su je a ga, suna ƙananan littafai, ko kunyar kasa karanta harrufan Alƙur’ani. Da yawa irin wannan kunyar na hana su zuwa karatu, ko da sun fara, sai su watsar.

Babu wata falala da Ubangiji zai ma a rayuwa, fiye da ka fahimci addini (Sahih Muslim, 1037).

1. Ka nemi malamin da zai jure warkar da kai, domin a matakinka, ba kamar ƙaramin yaro ba ne. Sai malami nutsattse mai haƙuri, da iya lallami. Ya baka lokaci, da tsara ma duk karatun da ya dace da kai, da za ku riƙa ‘darasu’ akai-akai. 

Ka sa iklhasi, ƙoƙari da kwazo, da jajircewa, da mallakar kayan karatu, da bibiyar malaminka, da ɗaukar lokaci, BA GAGGAWA (Diwan Imam Ash-Shafi’i, p. 109).

2. Idan ba ka iya haɗa baƙaƙen Larabci ba, yi ƙoƙarin ka koya, don karatun Alƙur’ani zai ba ka wahala sosai, haka ma sauran darussa. 

‘Baghadadiyya’ ko ‘Nurul Bayan’ kusan sune littafan koyon haɗawa da tada baƙin Larabci a yau. Idan ka kammala, ka fahimta, ka iya, malaminka zai sa ma littafin 'Tajwidi', da na ‘nahwun’ Larabci gwargwadon yadda ya fahimci fahimtarka.

3. Ka maida hankali kan koyon Alƙur’ani, domin shi ƙofa ce ta ilimin addini. Saboda girma, da uzuran rayuwa, kar kana ɗaukar karatun da za ka takura, har ka gajiya da wuri. 

Idan ma za ka iya, koda a kowacce rana ne, ka riƙa ɗaukar aya 1. Da wannan ɗaya-ɗayan, a shekara mai kwana 360, kana da Fatiha, Baƙara da ayoyi 67 na Ali-Imran, (Izu 5 da 1/2 kenan). Da a ce a shekarun baya ka fara, zuwa yanzu izunka nawa?

Za ka sauƙe Alƙur'ani, idan za ka yi:

• Aya 1 a kullum, shekara 17, wata 7 da kwana 9
• Aya 2 a kullum, shekara 8, wata 9 da kwana 18
• Aya 3 a kullum, shekara 5, wata 10 da kwana 13
• Aya 4 a kullum, shekara 4, wata 6 da kwana 24
• Aya 5 a kullum, shekara 3, wata 6 da kwana 3
• Rabin shafi a kullum, shekara 3, wata 4 da kwana 24
• Shafi 1 a kullum, shekara 1, wata 8 da kwana 12
• Shafi 2 a kullum, wata 10 da kwana 6
• Rubu’ (1/4) na izu a kullum, wata 8 cif (kwana 240)
• Nisfi (1/2) na izu a kullum, wata 4 cif (kwana 120)
• Hizbi a kullum, wata 2 cif (kwana 60)
• Juzu’ a kullum, wata 1 cif (kwana 30)

Idan ma za ka iya, za ka iya haddace Alƙur’ani a shekara 1, da haddar ayoyi 20, ko shafi 2 na Alƙur’ani Maigirma a kullum. 

4. AƘIDA:
‘Muƙarara’ ko ‘Usulus Salasa’, ko wani littafin ‘Tauhidi’ da malaminka ya ga dacewarsa da kai.

4. FIƘHU: 
A matakin farko, ka fara da ‘Ahlari’. Ahlari bai yi wa yara girma ba, bai kuma yi wa manya ƙarami ba, saboda tarin fa’idoji da suke cikinsa.

Idan ka cire gabatarwa, a cikin Ahlari akwai fasali 16, a ƙasan wasu fasulal, akwai bayanai a dunƙulallu, ko kashin wasu bayanan. Kowannen ka ba wa malaminka haɗin kai, ku bi su daki-daki, idan a kullum za ka ɗau karatun ‘Ahlari’, cikin wata 1 zuwa 2, za ka iya kamala shi. AMMA KAR KA YI GAGGAWA!

Bayan ka kammala, malamin zai sa ma wani littafin da ya dace, gwargwadon yadda yake fahimtar kana fahimtar karatun.

5. HADISI:
‘Arba’una hadisi’ ko wani, kamar ma Nawawin, yana da fa’ida sosai, kusan kowanne hadisi yana da ‘ƙa’ida azima’ (wani saƙo muhimmi).

Idan a kowanne sati za ka ɗauki karatun hadisi 1, za ka yi wata 8 da ½. Idan kuma kullum ne, a kwana 42 ne za ka kammala.

Ka dai yi gwargwadon yadda ba za ka gajiya ba, ba tare da harkokinka sun tsaya ba. Ka maye lokutan sharholiyya da lokacin bitar karatu, jin kaɗe-kaɗe ka maye su da sauraron karatu, ko darasi ko wata lakca mai fa'ida. A hankali za ka tara karatu mai yawa. A izinin Ubangiji, albarkacin neman ilimi da kyakkyawar niyya, sai ka ji wata nutsuwa da gamsuwa a cikin zuciyarka. 

✍️ Aliyu M. Ahmad
15th Rabi’ul Awwal, 1444AH
11th October, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #MusulunciDaRayuwa

Post a Comment

0 Comments