GUZURIN RAMADAN IX: RUKUNIN AZUMI NA FARKO (NIYYA)



MA’ANAR NIYYA

Niyya ararriyar kalmace daga yaren Larabaci wato "نية" ko "نوى"; wanda take nufin ‘KUDIRI’ a Hausance; ma’ana ‘kudurce son yin wani abu’ ko ‘kudurce son aikata wani abu’; Ibn Manzur: Lisal al-Arab shafi na 4980 (15/347); Mawrid p. 1196; Hanr Wehr p. 1032.


DALILIN/HUJJA GAME DA NIYYA

An ruwaito Hadisi daga Umar bn Khattab; Sahih al-Bukhari Hadisi mai lamba ta 1, 54, 2529, 6689 da kuma 6953; Muslim, 1907; Muwatta, 983; Abu Dawud, 2201; Ibn Majah, 4227; Tirmidhi, 1647; Nisa’i, 75, 3437 & 3794. Wanda yake cewa:

"إنما الأعمال بالنيات"

Fassara:
“Aiyuka suna tabbatuwa ne da niyya…”

Fadin Allah (S.W.T) cikin Suratul Bayyinat aya ta 5:

مَآ أُمِرُوٓاْ إِلَّا لِيَعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ حُنَفَآءَ

Fassara:
“Kuma ba a umurce su da komai ba face su bauta wa Allah, su na masu tsarkake addinin gare Shi...” - Bayyinat aya ta 5:

Fadin Allah (S.W.T.): Zumar aya ta 11:

قُلۡ إِنِّىٓ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱللَّهَ مُخۡلِصًا لَّهُ ٱلدِّينَ ۝

Fassara:
“Ka ce, Lallai ni, an umurce ni da in bauta wa Allah, ina (mai) tsarkake addini a gare Shi” - Zumar aya ta 11:


MUHALLIN NIYYA

An karbo hadisi daga Abu Hurairah, Sahih Muslim hadisi na 6708; Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:

"إن الله لا ينظر إلى صوركم وأموالكم، وإنما ينظر إلى قلبكم وأعمالكم"

Fassara:
“Lalle Allah baya duba izuwa surorinku da dukiyoyinku, (sani dai) Allah Ya na duba ne izuwa zukatanku da aiyukanku” - Sahih Muslim hadisi na 6708

A karkashin sharhin hadisi 1, hadisin Umar bin Khattab, أبى عبدالله محمد يسرى a cikin littafinsa "الجامع في شرح الأربعين النووي" juzu’i na farko (1) shafi na 48 bugun gidan "دار اليسر" Ya ce:

النية عمل من الأعمال قلوب

Fassara:
“Niyyar tana daga cikin aiyukan zuciya”

Imam An-Nawawi cikin "عمدة القاري" 1/23:

"النية قصد، وهو عزيمة القلب"

A takaice, niyyar Azumi ana kudurinta ne a zuciya, ba a bi sa harshe ba (furuci).


SHARUDDAN NIYYAR AZUMI

1. Yin niyyar (kudurta) daukar azumin Ramadhan, ba tare da kokonto ba (Misali: ko nayi azumin nan ko na fasa); sannan

2. Niyya ta Kasance a daura ta da niyyar Azumin Ramadana

3. Kwana da niyya tun dare ko kuma kafin fitowar Alfijir idan a Azumin Farillane (ie. Ramadhan); kamar yadda ya zai zo a Hadisin da za a kawo a kasa na jaddada niyyah. Sai dai an yi rangwame a Azumin Nafila.
.

JADDADA NIYYAR AZUMI

An ruwaito Hadisi daga Nana Hafsa bint (R.A.) Sunan Nasa’i hadisi na 2344:

"من لم يبيت الصيام قبل الفجر فلا صيام له"

Duk wanda bai kudurci Azumi kafin Alfijir ba, ba shi da Azumi”
- Sunan Nasa’i hadisi na 2344


TABBATUWAR NIYYA

Niyyar Azumi tana tabbatane a yayin da mutum ya kudurta a zuciyarsa, tun daga dare har izuwa kafin fitowar Alfijir da niyyar zai azuminci wannan ranar.


__________
To be continued …. in sha Allah


21st Sha’aban, 1438 AH
(18th May, 2017 AD)


Post a Comment

0 Comments