GUZURIN RAMADAN V : FALALAR AZUMI


Azumi (sawm) ibada ce mai tarin falala a zahiri da badini, daga ciki akwai karin samun kusanci zuwa ga Allah, nutsuwa, tarbiyya kai, karin lafiya, ga kadan daga cikin falaloli da Allah (S.W.T.) Ya bawa ibadar Azumi:


KARIN SAMUN TAQWA, DAIDAITA TARBIYYA, NESAN MIYAGUN AIYUKA

Allah (S.W.T.) Ya fadi a cikin Alkur’ani; Suratul Baqra aya ta 183:

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡڪُمُ ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِڪُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ ۝
.
“Ya ku wadanda kuka yi imani! An wajabta azumi akanku, kamar yadda aka wajabta shi akan wadanda suka gabaceku, fatan KU SAMI TAQWA


An karbo hadisi daga Abdullahi (R.A.); Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:

"يا معشر الشباب، من استطاع الباءة فليتزوج، فإنه أغض للبصر وأحصن للفرج. ومن لم يستطع فعليه بالصوم فإنه له وجاء."

Fassara:
"Yaku taron matasa, duk wanda ya sami dama yayi aure, to yayi; saboda shi (aure) yana taimakawa wajen kiyaye kallace-kallace, yana kuma kare mutunci (daga fadawa cikin mu’amalar banza i.e. zina); ga wanda ba shi da ikon na yin aure, sai ya rika yin azumi, saboda shi azumi yana rage sha’awa” – Bukhari hadisi na 5066

Azumi yana da mutukar muhimmanci wajen tsarkake zuciya akan bin Allah, yana tarbiyantar da mai azumi kan bin dokokin Allah da nisantar saba masa wajen aikata aiyukan da ya haramta, musamma idan mai azumi ya san aikata za su bata masa ibadarsa ta azumi.

Misali; mutum yana azumi zai kasance yana cikin jin yunwa, kishirwa, yana kuma son yayi hirar duniya, ga sha’awar mata, amma saboda da jin tsoron Ubangiji sai ya hakura har izuwa lokacin da aka kayyade masa (Baqara: 187).


AZUMI BABBAR IBADA CE DA BA TA DA IYAKANTACCEN LADA

An hadisi daga Abu Umamah (R.A.), cewa Ya tambayi Manzon Allah (S.A.W.):

"أي العمل أفضل؟"

“Wanne aikine yafi (falala/daraja)?; (sai) Manzon Allah (S.A.W.) Yace:

"عليك بالصوم فإنه لا عدل له".

Fassara:
“Ka riki azumi,domin babu wani (aiki) da yayi daidai da shi” – Nisa’i hadisi na 2224

A wata ruwaya ta Abu Hurairah (R.A.); Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:

"قال الله: كل عمل ابن آدم له إلا الصيام فإنه لي، وأنا أجزي به، والصيام جنة...".

Fassara:
“Allah (S.W.T.) Ya ce: ‘Dukkan aiyukan dan Adam nasa ne ban azumi, saboda shi Azumi nawane, kuma ni na ke bayar da sakayyarsa, kuma azumi garkuwane…” (Bukhari, hadisi na 1904).


GARKUWA DAGA WUTA

An karbo hadisi daga Mutarrif (R.A.) Yace: “na shige wajen Usman bin Abi Al’As, sai ya nemi ya kawo min madara/nono, sai na ce masa ‘Ni mai azumi ne’. Sai ya ce min: “Na ji daga Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:

"الصيام جنة من النار، كجنة أحدكم من القتال"

Fassara:
“Azumi garkuwa ne, kamar/tamkar yadda garkuwar dayanku (ta ke kareshi) a filin yaki” - Nasa’i  hadisi na 2233

An karbo hadisi daga Abu Hurairah (R.A.), cewa Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:

"من صام يوماً في سبيل الله زحزحه الله عن النار سبعين خريفاً"

Fassara:
Duk wanda ya azumci rana saboda (neman kusanci ga) Allah; Allah nisanta  shi da wuta da tsawon tafiyar shekara saba’in”- Tirmidhi, 1622; Ibn Majah, 1718

A ruwayar Abu Sa’id Al-Khudry (R.A.); Jami’at Tirmidhi hadisi na 1623:

"لا يصوم عبد يوما في سبيل الله إلا باعد ذلك اليوم النار عن وجهه سبعين خريفا"

Fassara:
“Babu wani bawa da zai yi azumi a wata rana saboda Allah; face Allah ya nisanta fuskarsa daga wuta da tsawon tafiyar shekara saba’in” - Jami’at Tirmidhi hadisi na 1623


ADDU’AR MAI AZUMI KARBABBIYA CE

An karbo hadisi daga Abdullahi bin Amr’ bin ‘As (R.A.), cewa Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:

"أن للصائم عند فطره دعوة لا ترد"

Fassara: “Addu’ar mai azumi a yin buda baki bata dawowa (ma’ana ta tafi kenan, za a kuma karba)” - Ibn Majah 1753


SAMUN DARAJA TA MUSAMMA A RANAR ALKIYAMA/ALJANNA

An kabo hadisi daga Sahl (R.A.); Manzon Allah (S.A.W.) Yace:

"إن في الجنة بابا يقال له: الريان، يدخل منه الصائمون يوم القيامة، لا يدخل منه أحد غيرهم، فإذا دخلوا أغلق، يقال: أين الصائمون؟ فيقومون لا يدخل منه أحد غيرهم، فإذا دخلوا أغلق فلم يدخل منه أحدٌ"

Fassara:
“Akwai wata kofa a Gidan Aljanna ana kiranta ‘Ar-Raiyan’, masu azumi su ne za su shige ta cikinta a Ranar Alkiyama, babu kuma wanda zai shige bayansu; Za a ce: ‘Ina masu azumi? Sai su mike (su shige), babu wanda zai shige face su. Bayan su shige za a rufe (kofar) babu kuma wanda zai shiga ta ita kofar” - Bukhari hadisi na 1896


SAMUN KARIN LAFIYA A JIKI

A bincike na masana lafiya; Azumi yana da amfani musamman wajen rage teba, nauyin jiki, daidaita gudun jini, warware hanjin ciki, daidaita narkewar abinci a cikin ciki dss. (Gerard; Principles of Human Anatomy p. 839; Maried et al, Human Anatomy p. 738; Marcia Adrews, Everything you need to know about diseases, 1996; Berkow et al, Merc Manual of Diagnosis and Therapy, 1997)

Sannan ana amfani da azumi wajen jinyar wasu cututtuka kamar cutar suga , ko karanci suga a jikin bil Adama (hypoglycemia), cututtukan da suka shafi huhu da hanyar iska (misali; pulmonaritis, aspiration pneumonia, LRTI dss); see Dr. Norman 17th April, 2003: Fasting before surgery – Health & Wellbeing; Sarah Knapton 5th June, 2014; Fasting for three days can regenerate entire immune system, study find: Telegraph.co.uk; 839


_________
To be continued… in sha Allah.


17th Shaaban, 1438 AH
(14th May, 2017 AD)


Post a Comment

0 Comments