GUZURIN RAMADAN II: FALALAR WATAN RAMADAN

Watan Ramadhan watane mai alfarma da falalar gaske, watane da Allah Ya bawa bayinsa domin su daidaita tsakaninsu da shi, watane da Allah Yake saukar da ni’ima, rahama, gafara, da nutsuwa ga bayinsa masu ibadar azumi. Ga dan takaitattun bayanai daga cikin daraja da falalar da Allah yayi watan Ramadhan:

1. KEBANCE SHI (RAMADHAN) DA YIN IBADAR AZUMI (DAYA DAFA CIKIN RUKUNAN MUSULUMCI) A CIKINSA

Watan Ramadhan shi ne watan da sharia ta sanya ya kasance a cikinsa za a gabatar da ibadar azumi ie. Sawm (Qur’an:2:182), shi kuma ‘azumi’ daya ne daga cikin  (أركان الإسلام)  rukunai ko ginshikai ko shika-shikai (asassu) na Addinin Musulunci kamar yadda a zo a Hadisin Abdullahi dan Umar (R.A.):

" بُنِيَ  الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ: شَهَادَةِ أَنْ لَا إلَهَ إلَّا اللَّهُ  وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ  الزَّكَاةِ، وَحَجِّ الْبَيْتِ، وَصَوْمِ رَمَضَانَ".
 .
“An gina Musulunci a bisa abubuwa guda biyar; 
1. Shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, (kuma) Annabi Muhammad Manzon Allah ne; da
2. Tsaida Sallah; da
3. Bayarda Zakkah; da
4. Ziyartar Dakin Allah Mai alfarma (Aikin Hajji); da
5. AZUMTAR WATAN RAMADANA; Bukhari (8, 4515); Muslim (16); Tirmidhi (2609); Nasa’i (5001), Ibn Majah (158, 1336).

Sannan Allah (S.W.T.) Ya fadi a cikin Alkur’ani; Suratul-Baqara aya ta 185:

شَہۡرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِىٓ أُنزِلَ فِيهِ ٱلۡقُرۡءَانُ هُدًى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَـٰتٍ مِّنَ ٱلۡهُدَىٰ وَٱلۡفُرۡقَانِۚ فَمَن شَہِدَ مِنكُمُ ٱلشَّہۡرَ فَلۡيَصُمۡهُۖ

Ma’ana:
“Watan Ramadan shine wanda aka saukar Al-Qur’ani a cikinsa domin shiriya ga Mutane, tare da bayani mai rarrabe tsakanin gaskiya da karya, DUK WANDA YA HALARCI WATAN DAGA CIKINKU YA AZIMCE SHI…”


2. RAMADHAN SHI NE WATAN DA AKA SAUKE ALKUR’ANI A CIKINSA

Kamar yadda ya zo a cikin Al-Qur’ani, Suratul Qadr aya ta 1; Suratud Dukhaan aya ta 3, da Suratul Baqarah aya ta 185, a cikin shi wannan wata (ie. Ramadhan) Allah (S.W.T.) Ya sauke Alkur’ani Maitsarki, wanda shi ne kundi kuma jagora wajen sanin hakikanin shariar Allah. Allah (S.W.T.) Ya ce:

شَہۡرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِىٓ أُنزِلَ فِيهِ ٱلۡقُرۡءَانُ هُدًى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَـٰتٍ مِّنَ ٱلۡهُدَىٰ وَٱلۡفُرۡقَانِ

Fassara:
“Watan Ramadan shine wanda aka saukar Al-Qur’ani domin a cikinsa domin shiriya ga Mutane, tare da bayani mai rarrabe tsakanin gaskiya da karya…” (Baqara, aya ta 185)

إِنَّآ أَنزَلۡنَـٰهُ فِى لَيۡلَةٍ مُّبَـٰرَكَةٍۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ ۝

Fassara:
Lallai ne Mu, Muka saukar da shi a cikin dare mai albarka (Lalaitul Qadr). Lallai Mu, Mun kasance Muna yin gargadi” (Dukkhaan, aya ta 3)

إِنَّآ أَنزَلۡنَـٰهُ فِى لَيۡلَةِ ٱلۡقَدۡرِ ۝

Fassara:
“Lallai ne Mu, Mun saukar da shi (Alkur’ani) a cikin Lailatul Qadr (dare mai daraja).” (Qadr, aya ta 1)


3. SAUKE RAHAMA, KANKARE ZUNUBIN MASU IMANI DA NINNINKA LADAN IBADA

Yana daga cikin Falalar Ramadan, bude kofofin rahama, kankare zunubin masu imani da ninninka ladan ibada, kamar yadda aka karbo Hadisi daga Abu Hurairah (R.A.), Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:

"إذا جاء رمضان فتحت أبواب الجنة"
.        
Fassara:
“Idan Ramadhan ya zo, ana bude kofofin Aljanna” (Bukhari, 1898)

A cikin wata ruwayar ta Abu Hurairah (R.A.) Sahih al-Bukhari hadisi na 1901, Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:

…”مَنْ قَامَ رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ

 Fassara:  
“…Duk wanda yayi tsayuwa a (kwanakin) Ramadhan, yana mai imani da neman lada an gafarta masa abin da ya gaba na zunubinsa” (Sahih al-Bukhari, 1901)

A wata ruwayar ta ita ma ta Abu Hurairah; Annabi (S.A.W.) Yace:

"... رمضان إلى رمضان مكفرات لما بينهن ..."
.
Fassara:
“…Ramadan zuwa Ramadan Kaffarar abin da ke tsakanin su ne…”
(Sahih Muslim, 574)

Yana daga cikin Falalar Ramadhan, Allah yana tsamar da wadanda suka cancanci shiga wuta su koma Aljanna; Musnad Ahmad 5/256.

Yana daga cikin Falalar Ramadha, Duk wanda ya Azumci watan Ramadhan sannan ya Azumci kwanaki shida a Shawwal, kamar ya Azumci shekara ne; Annabi (S.A.W.) Ya ce:

"من صام رمضان وأتبعه ستا من شوال كان كصيام الدهر"
(Sahih Muslim, 822)

Yana daga cikin Falalar Ramadhan, Duk wanda ya yayi Umrah za a bashi lada tamkar yayi aikin Hajji; Hadisin Ibn Abbas a cikin Sahih Muslim hadisi na 3097; Tirmidhi, 939; Ibn Majah, 2991:

"فإذ جاء رمضان فاعمتري فإن عمرة فيه تعدل حجة"

Yana daga cikin falalar Ramadan samun farin ciki da nishadi lokacin Sahur da kuma Buka baki (iftar) ba’a samun irin wannan a wani lokacin bayan Ramadhan (sai ga wadanda suke yin Azumin nafila a sauran kwanaki). Allah Yana bayarda gwaggwaban lada ga wanda ya ciyar da mai azumi ko da barin-dabino ne (Tirmidhi, 807) wannan ma ibadace da aka fi yinta a Ramadhan; Watane na Tilawar Alkur’ani Maitsarki (Bukhari, 5);  Watane na yin ibadar Ittikafi, yawaita Azkar da sauran ibadu.


4. GYARAN TARBIYYA

Watan Ramadhan tamkar wani zamani/lokacine da mutane ke shiga domin daukar darasi (course) na yadda za su gyara zukatansu, mu’amalarsu tsakaninsu da Mahalicci (Allah) da kuma ‘yan uwa da abokan zama.

Sannan watane da yake nisanta mutane daga aikata aiyukan sabon Allah, kame harshe daga yarfaffun zantuka, fada ko musu da juna da sauransu, kamar yadda ya zo cikin Sahih Bukhari hadisi na 1904:

"...وإذا كان يوم صوم أحدكم فلا يرفث ولا يصخب، فإن سابه أحد أو قاتله، فليقل: إني امرو صائم."

Sannan a lokacin Ramadhan kowa-da-kowa ke kokari da dagewa wajen yawaita ibadu, azkar, sada zumunta, sadaka da sauran aiyuka nagari domin neman kusanci da Allah.

Suratul Baqara aya ta 183:

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡڪُمُ ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِڪُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ ۝
.
“Ya ku wadanda kuka yi imani! An wajabta azumi akanku, kamar yadda aka wajabta shi akan wadanda suka gabaceku, fatan KU SAMI TAQWA”


5. SAMUWAR LAILATUL QADR (DARE MAI DARAJA) A WATAN RAMADHAN

Samuwar Lailatul Qadr a cikin watan Ramadhan shi ma wata daraja da Allah karrama wannan wata da ita, kuma yana karawa watan falala-kan-falala. Kamar yadda Allah (S.W.T.) Ya sauke surah sukutum wacce take bayyana darajar wannan dare:
              
بسۡمِ ٱللهِ ٱلرَّحۡمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ ۝ إِنَّآ أَنزَلۡنَـٰهُ فِى لَيۡلَةِ ٱلۡقَدۡرِ ۝ وَمَآ أَدۡرَٮٰكَ مَا لَيۡلَةُ ٱلۡقَدۡرِ ۝ لَيۡلَةُ ٱلۡقَدۡرِ خَيۡرٌ مِّنۡ أَلۡفِ شَہۡرٍ ۝ تَنَزَّلُ ٱلۡمَلَـٰٓٮِٕكَةُ وَٱلرُّوحُ فِيہَا بِإِذۡنِ رَبِّہِم مِّن كُلِّ أَمۡرٍ ۝ سَلَـٰمٌ هِىَ حَتَّىٰ مَطۡلَعِ ٱلۡفَجۡرِ ۝

1. Lallai ne Mu, Mun saukar da shi (Alkur’ani) a cikin Lailatul Qadr (dare mai daraja).
2. To, me ya sanar da kai abin da ake ce wa Lailatul Qadr (dare mai daraja)?
3. Lailatul Qadr shine mafi alheri ne daga wasu watanni dubu.
4. Mala’iku da Ruhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu daga kowane umarni.
5. Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri.

Annabi (S.A.W.) Yace:

"مَنْ قَامَ ليلة القدر إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ"

"Duk wanda yayi tsayuwa a Daren Lailatul Qadr, yana mai imani da neman lada an gafarta masa abin da ya gaba na zunubinsa…"
(Hadisin Abu Huraira  a cikin: Sahih Bukhari, hadisi na 1901)

ABIN LURA!
Falalar Watan Ramadhan ba za ta kidayu ba, sai dai domin a qaranta rubutu saboda da abin da Larabawa suke cewa: “MAFI ALKHAIRIN ZANCE; SHI NE WANDA YA TQAITA KUMA YA SHIRYAR.”


______________
To be continued… in sha Allah.


16th Shaaban, 1438 AH
(11th May, 2017 AD)

Post a Comment

0 Comments