Ramadan yana tabbata ne ta hanyoyi guda biyu (2); wadannan hanyoyi sune:
1. Ganin Wata; ko idan
2. Watan Sha'aba ya cika kwanaki 30
1. GANIN WATA
Kamar Yadda Allah (S.W.T.) Ya fadi cikin Al-Qur’ani Mai Girma; Suratul Baqarah aya ta 185:
ۚفَمَن شَہِدَ مِنكُمُ ٱلشَّہۡرَ فَلۡيَصُمۡه
Fassara:
"...duk wanda ya halarci watan (Ramadhan) daga cikinku ya azumce shi.."
Hakanan karbo Hadisi daga Abdullahi bin Umar (R.A.), daga Manzon Allah (S.A.W.) Yace:
"الشهر تسع وعشرون ليلة، فلا تصوموا حتى تره، فإن غم عليكم فأكملوا العدة ثلاثين"
Fassara:
“Wata yana da kwanaki ashirin da tara (29); Kada ku dauki Azumi har sai kun ga shi (wata), idan an rufe muku shi, to ku cika adadin talatin.” - Sahih al-Bukhari hadisi na 1907). Sannan Abu Hurarih ma ya ruwaito makamancin wannan Hadisi a Sunan an-Nasa’i hadisi na 2119.
ABIN NUFI; watan yana juyawane a cikin kwanaki 27 da awannani 7 da mintuna 43 da sakan 11.5 daga inda yake a sama. Amma mu anan duniya munaganinsa a cikin kwanaki 29 da awanni 12 da mintuna 44; shi ne ake ce masa ‘Lunar Month’ kamar yadda masa harkar taurari (Astronomer) suka tabbatar (Spudis, Paul D. "Moon." Microsoft® Student 2009 [DVD]; Clabon Walter & Arthur Cox (2000) Astrophysical Quantities p. 308). Annabinmu Yayi gaskiya (S.A.W.).
Saboda haka idan kuma ba’a ga watan ba a cikin kwanakinsa na 29 ba, saboda dalili na gajimare/girgije, hadari ko wani dalili, sai a kirge kwanakinsa su cike talati (30) sai a dauki Azumi, shikenan Ramadan ya soma.
MATSAYIN GANIN WATA NA MUTUM DAYA KO MUTANE BIYU (2) A CIKIN AL’UMMA
Sannan ba dole sai kowa-da-kowa ya ga wata ba ne ake daukar Azumi, matukar an sami mutum daya zuwa biyu zuwa sama amintattu, balighai, masu hankali ya wadatar da al’ummar Musulmai su dauki azumi bayan tantancewa da tabbatarwa daga shuwagabanni Musulmai (i.e. Yan kwamatin duban wata da Fadar Sarkin Musulmai), saboda da wani Hadisi na Abdurrahman bn Zaid bn Khattab da yake cewa:
أنه خطب الناس فى اليوم الذى يشك فقال ألا إنى جالست أصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم، وساءلتهم وأنهم حدثونى أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: "صوموا لرؤيتة وأفطروا لرؤيته وانسكوا لها فإن غم عليكم فأتموا ثلاثين، وإن شهد شاهدان فصوموا وأفطروا".
:Fassara
“(Abdurrahaman bn Zaid (R) ya yi wa mutane khutuba ranar da ake shakkar kamawar watan Ramadan (ie. 29 Sha’aban) sai yace: Ku saurara! Lallai ni na zauna da sahabban Manzon Allah (S.A.W.) kuma na tambaye su suka ba ni labari cewa Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce: “Ku yi azumi idan an ga jaririn wata (hilal), kuma ku sha, ku yi yankan layya idan an ganshi, amma idan aka rufe muku ganinsa ku cika talatin, idan (kuma) shaidu biyu (2) suka shaida to ku yi azumi, kuma ku sha ruwa” - Nasa’i Hadisi na 2118).
Hakanan an ruwaito hadisi daga Abdullahi bin Umar a cikin Sunan Abu Dawud hadisi na 2342 inda yake cewa:
تراءى الناس الهلال فأخبرت رسول الله صلى الله عليه وسلم أني رأيته، فصام وأمر الناس بصيامه
Fassara
Mutane sun yi kokarin ganin wata, sai na larabtawa (fadawa) Manzon Allah (S.A.W.) cewa ni na gan shi (watan); sai (Manzon Allah [S.A.W.]) Ya dauki azumi kuma ya umarci mutane (su ma) su dauka
DAGA MAGABATA:
Imam Abu Hanifa, Imam as-Shafi’i sun
tafi akan idan Mutum guda daya Adali ya
ga wata, in har an tabbatar da ganinsa
to a dauki Azumi, dogaro da Hadisin Abdullahi bin Umar wanda yake cikin Sunan
na Abi Dawud No. 2342 da yake sama.
Sannan kuma Imamu Maliku, Sufyan al-Thauri da Imam al-Au’azi su
kuma sun kan sai dai in mutum biyu ne suka ga wata tukun jama’a za su dau Azumi,
saboda hukuncin bada sheda, Suratul Talaq aya ta 2:
…وَأَشۡہِدُواْ ذَوَىۡ
عَدۡلٍ مِّنكُمۡ…
Wasu daga cikin Magabata (Malamai) sun tafi akan cewa, ana iya
daukar Azumi da ganin mutum daya wanda yake Adali kamar yadda yake a a Hadisin
Abdullahi bn Umar, Mazhabar Abu Hanifa da Imamu Shafi’i, da kuma umarnin
shugaba kan hakan.
Wasu kuma suna kan Hadisin Abdur-Rahman bn Zayd wanda akan fitar a
Sunan Nisa’i (2116) na sai an sami shaidar mutum biyu, adalai.
AMFANI DA KALANDA (CALENDAR)
Gani da idanu kuru-kuru, ko cikar Sha’aban kwanaki talati, sune hanyoyi da Sharia ta tanada mana domin tabbatar da watan Ramadan, sau da yawa ana samun sabani ko kuskuren kirge a mafi yawancin lokuta tsakanin ganin wata da lissafin kalanda, don haka domin tabbatar da wata ba’a amfani da kalanda (Qurtubi: Al Jami L’ahkamil Qur’an 1/363; Fatul Bari 4/127; Hashiyat ad-dusuki ‘Alash sharhil Kabeer, 1/510)
2. CIKAR SHA’ABAN KWANAKI TALATIN (30)
Kamar yadda ya zo a hadisin sama na Abdullahi bin Umar R. (Bukhari, 1907), idan aka duba wata a ranar 29 ga watan Sha’aban ba ganshi ba kwata-kwata, ko kuma gajimare, girgije, hadari sun rufe sama, sannan kuma ba’a sami wasu wadanda suka ce sun gani ba, to sai a cika kwana na 30 ga watan Sha’aban, a washegari 30 ga Sha’aban sai a tashi da azumi, kamar yadda ya zo a daya ruwayar:
" فإن غم عليكم قدورا له."
Fassara:
“Idan an boye muku (watan),
to ku cika shi (ma’ana kwanaki talati)” (Bukhari, 1906)
YADDA AKE DUBAN WATA
Ya kamata ‘yan kwamatin ganin wata, da sauran al’ummar Musulmai su
fara duban wata a ranar 29 kidayar kwanakin watan Sha’aban, ciki da wajen gari,
musamma wajen da yake da sarari babu dogayen gine-gine, kuma inda yake babu
girgije a saman.
Ana duba wata dab da faduwar rana, a dai-dai ko kusa da inda rana
take faduwa ne (yamma), kasa-kasa.
Sannan yana da kyau a lura, a ranar duban farko; wata baya dadewa
yake bacewa, da an gani a gaggauta neman samun shaidu masu yawa daga cikin al’ummar
Musulmai.
Da zarar an ganshi ayi kokarin sanar da limamin ko maiunguwa à Hakimi à
Sarki à
Sarkin Musulmai domin a tabbatar a kuma sanar da inda basu ganiba, saboda
girgije ko hadarin ruwa da ya yi musu hijabi da ganin wata.
A karshe, babu mai bada izinin/umarni da dauki azumi sai Sarkin
Musulmai (Sources: Guide for the Moon Sighters; JNI Sokoto: 1438 AH/2012)
ADDU’A YAYIN GANI JARIRIN WATA
Duk wanda Allah Ya bashi ikon ganin wata, yana da kyau ya karanta
wannan addu’a, kamar yadda Abdullahi dan Umar ya ruwaito (Sunan as-Darimi
hadisi na 1740); cewa Annabi (S.A.W.) Ya kasance idan ya ga jaririn wata Yana
cewa:
اللَّهُ أَكْبَرُ، اللَّهُمَّ أَهِلَّهُ
عَلَيْنَا بِالأَمْنِ وَالإِيمَانِ، وَالسَّلامَةِ وَالإِسْلامِ، وَالتَّوْفِيقِ
لِمَا تُحِبُّ رَبَّنَا وَتَرْضَى، رَبُّنَا وَرَبُّكَ اللَّهُ
Hausar Arabiyya (Transliteration):
Allaahu 'Akbar, Allaahumma 'ahillahu 'alayna bil'amni wal'eemaani,
wassalaamati wal-'Islaami, wattawfeeqi limaa tuhibbu Rabbanaa wa tardhaa,
Rabbunaa wa Rabbukallaahu.
Fassara:
“Allah Maigirma, Ya Allah! Ka sanya tsayuwarsa a gare mu ta zamo
kwanciyar hankali ce da imani, da aminci da musulunci, da kuma gamonkatar da
abin da Ka ke so, Ya Ubangijinmu, kuma Ka ke yarda da shi. Ubangijinmu da
Ubanjinka (ya kai wannan jaririn wata!) shi ne Allah" - Sunan as-Darimi hadisi na 1740.
_________
To be continued… in sha Allah.
15th Shaaban, 1438 AH
(12th May, 2017 AD)
0 Comments