HAUSA: KUSKURE WAJEN RUBUTA SUNAN ALLAH


Taƙaitaccen bayani game da kuskure wajen rubuta sunan Allah, musamman Social Media (i.e. Facebook, WhatsApp, Telegram etc).

Allah sunane sannanne kuma keɓantacce a dukkan yaruka (languages) da addinan (i.e. Proper Noun), na abin bautar addinan Abrahamic.

Shi kuma Proper Noun (keɓantaccen suna/sunan yanka), kamar yadda muka sani, yana daga cikin dokokin rubutu; a duk yayi da zamu rubuta keɓantaccen suna mu fara shi da BABBAN BAƘI (capital letter/uppercase letter/majuscule) idan salon rubutu a ƙananan baƙaƙe (miniscule form) zamuyi.

Ko ba a addinance ba, ƙuskurene babba ga kowa, ko da ko mutum ba Musulmi bane, ko ba Banasare ko Bayahude bane. Kai ko kai sheɗanne idan ka zo rubuta sunan Allah a ƙa'ida fa to sai ka fara da BABBAN BAƘI (capital letter), saboda sunan PROPER ne.

TABBATAR DA SUNAN "ALLAH" A MATSAYIN KEƁANTACCEN SUNA (PROPER NOUN)

Allah, Shi ne Ubangiji abin bauta a addinan da suka yarda/imani da risalan Annabi Ibrahim A.S. (Abrahamic Religion) i.e. Islam 🌙️ (Musulunci), Christianity ✝ (Kiristanci/Nasara) da Judaism ✡ (Addinin Yahudawa).

Allah (S.W.T.) Shi ne Maƙagin halittar alam (dukkan halittu) [Q:Al-Fatiha:2, Al-Aaraf: 53], Masanin ghaibu [Q:Al-Hashir:22], Sarki Mai hisabi a ranar sakamako [Al-Fatiha: 4] dss.

Ba'a taɓa samun wani ya keɓanta da wannan suna ba, wa lau a da ko a yanzu, idan aka ce ALLAH, kowa yasan ubangiji/abin bautar addinan Abrahamic ne. Kamar yadda Sikkh kowa yasan IK Onkar suke bautawa, haka ƴan addinin Hindu suna da ababen bauta dubbai mafiya shahara Halebidu, Brahma, Shiva, Vishnu, Ganesha dss. Hakanan ƴan Buddhism suna bautawa gunki Budha, ko Saumya, Rauhineya ko Tunga.

To ko sunan waɗannan gumakan/ababen bautar sauran addinai za a rubuta ana farawane da manyan baƙaƙene, balle namu Allah na gaskiya.

Don haka kuskurene ka rubuta sunan kamar haka: allah; sai dai ka rubuta shi  Allah ko ALLAH. harafin farkon (a) babba ake rubutata (A) sai ka following sauran harafan da ƙanana (llah). A + llah = Allah.

Har a wajen sauran Sunaye da Siffofin Allah ma, ana capitalizing harafin farkone (initial letter), misali: Mairahama, Babban Sarki, Maƙagi, Masanin ghaibu etc/dss.
.
Sa'annan ko da wajen rubuta lamiri/waƙilin suna (Personal Pronoun) wanda ake son jinginawa Allah, to yana da kyau shi ma mu riƙa capitalizing harafin farko (initial letter).

Misali:
Allah Yasa mu dace.
Allah Ya amsa.
Allah Shi ne mai yadda Yaso.

NB: Wannan YA da SHI ɗin harafan farkonsu (initial letters) da babban baƙi (capital) ake rubutawa.

Allah Yasa mu gyara.

Aliyu M. Ahmad
Sat. 26th J/Akhir, 1438 AH
(25th March, 2017 CE)

Post a Comment

0 Comments