Phone Master 🛡️


Kafin na fara bayani wannan manhajar (app), ina son mu sani, wayoyin TECNO, INFINIX and ITEL uwarsu ɗaya, ubansu ɗaya, duk subsidiary ne na babban kamfani ‘Transsion Holdings’ dake China, har da ‘accessories’ (kayan waya) na Oraimo, da kamfanin gyaran waya na Carlcare, duk tushensu ɗaya. 

Idan ma muka lura da OS (Operation System) na Tecno, HiOS, da XOS na Infinix, duk za mu ga 'features' ɗaya ne, na Shalltry Group, ciki har da 'PHONE MASTER', da Theme, da File Manager... Itel ce kawai ke amfani da Android Go (OS don wayoyi masu ƙaramin farashi).

Kusan duk mai amfani da wayoyin TECNO, INFINIX da ITEL na da PHONE MASTER a waya. Amma mun san amfanin shi? 

PHONE MASTER yana da:

1. Junk Cleaner 🧹
Yana goge duk wani tarkace na ‘caches’ da wayarka ta tara, wanda ke cinye ma 'space'.

2. Phone Cooler ❄️
A lokacin da wayarka ta ɗau zafi, ka yi amfani da ‘Phone Master’, zai rufe duk wani ‘app’ da ke sa wayarka ɗaukar ɗumi, daga nan zafinta zai ragu.
 
3. Phone Boost (Speed Booster) 🚀
Lokacin da ka ji wayarka ta ɗan yi nauyi, musamman masu 2, 3, 4GB RAM, yi amfani da ‘Phone Master’ don rage wa waya nauyi.

4. Power Saver 🔋
Idan ka buɗe wayarka, akwai ‘apps’ da ko ba buɗe su suna shan caji (on background), wannan ‘Phone Master’ zai ‘hibernating’ maka su, idan ka shiga ‘Power Saver’ don tattala ma cajin waya.

5. Data Saver 📱
Yana rufe ‘background apps’ masu shan ‘data’, waɗanda koda ba ka buɗe su ba.

6. Storage Cleaner 💾🧹
Lokacin da wayarka da cika, ka rasa me za ka goge ka samu 'space', to; ka buɗe ‘Storage Cleaner’ na ‘Phone Master’, zai ware ma ‘files’ masu nauyi (large file), rukuni-rukunin videos, photos, docs, apps; sai ka zaɓi na  gogewa, don ka samu ‘space’.

7. Freezer 📦
Za ka iya ɓoye wani ‘app’ daga wayarka, ya fice daga cikin ‘app menu’ baki ɗaya, kuma zai dakata da aiki (pause/force stop) ba tare da uninstalling (cire shi) daga wayarka ba, idan ka yi ‘freezing’ ɗinsa da ‘Phone Master’, har sai ka ‘unfreezing’ nasa zai dawo aiki.
 
Wannan zai yi amfani musamman ga masu yawan bayar da wayoyinsu, don tsare sirrinkan ‘chatting’, ‘SMS’ ‘email’… da sauransu.

8. App Locker 🔐
Za ka iya sa wa kowanne ‘app’ na wayarka ‘password’ da 'Phone Master', ciki har da ‘SMS’ da ‘contacts’ da ‘call history’.  

9. App Manager
Wannan kuma yana:
•  Uninstalling na ‘app’,
•  Re-installing na ‘app’,
•  Rufe notification na wasu ‘app’ ɗin, da kuma
•  Duba ‘app’ da aka yi amfani da shi a ƙarshe (sorted).

10. Antivirus 🛡️
Yana kare waya daga ‘file’ masu ‘virus’, ko dubawa da goge ‘file’ masu virus daga cikin waya.

11. Battery Management 🪫🔋
A wannan ana saita:

• Smart Charge 🔋🔌
Yana ‘battery optimization’, don hana waya cajin da ya fi ƙarfin buƙata (over charging). 

• Super Charging 🪫🔌
Dakatar da aikin wasu manhajoji, da ba wa batir damar saurin cika.

• Power Saving Mode 🪫
Don tattala cajin waya, musamman lokacin da ya kusa ƙarewa.

12. Block Unwanted Calls 📳
Ana iya sa lamba (contact) a ‘blacklist’, ta yadda, ko mutum ya ƙira layinka, ba zai shigo wayar ba.

13. Secure Browser 🌐
A cikin Phone Master, akwai browser wacce ba ta buɗe shafuka marasa tsaro (insecure webpages). 

14. File Mover 📤📥
Yana transfer na file daga SD/Memory Card, ko OGT zuwa waya, ko daga waya zuwa waɗancan ma’adanan, da sauri.

15. Mobile Daily 📊
Wannan yana duba:   

•  App Report – adadin lokacin da ka ɓata kan kowannen app a wayarka, mis. Social media.

•  Phone Status – yana nuna ‘storage space’ da RAM na cikin waya.

•  Usage Behaviour – yana nuna ‘screen usage’, tsawon lokutan da wayarka ke buɗe, ana amfani da ita.

Duk waxannan ‘features’ a cikin ‘Phone Master’ suke. Masu wayoyin Android na Tecno, Infinix da Itel su duba wayarsu, za su ga wannan manhajar.

Ana kuma iya ‘Phone Master’ shi a sauran wayoyin 'Android' (ban da iSO/iPhone) daga Playstore:
 https://bit.ly/2LkB5Hc

✍️ Aliyu M. Ahmad
3rd Rabi’ul Awwal, 1444AH
29th September, 2022CE

#AliyuMAhmad #FasaharZamani

Post a Comment

0 Comments