Proactivism



Ka san kana da wata matsala,
Ka san kana da wani rauni.

Wane mataki ka ɗauka domin shawo kan wannan matsalar taka? Wane mataki ka ɗauki domin disashe wannan rauni?

Misali:

Tunda ka shiga jami'a ajin farko, aka haɗa ku group presentation. Kuma ana son kowanne member a cikin wannan group ya yi magana a gaban aji (saboda a 'objective' na hakan, ana so ku san juna, ku kuma iya magana a gaban mutane).

Da aka zo kanka, sai:

1. Ka kasa magana a gaban mutane (jikinka na karkarwa, muryarka na rawa),
2. Turancin da kake bakinka akwai kusakurai, na nahwu (grammar) da furuci (pronunciation).

A ƙarshe, gulmarka abokan karatunka suke yi, wane ga gaye amma ba Turanci. Kuma kai ma a karan kanka ka san akwai wannan matsalar.

Kuma kullum a cikin zuciyarka kana ji, eh ba ka iya ba. Har ma kunya kake ji a zo wajen da za a yi magana da Turanci don kada ka kwafsa. RASHIN IYA TURANCI SHI NE 'WEAKNESS' ƊINKA.

• Tsawon shekara 4 da ka yi a jami'a, me kake da ba ka ɗauki matakin daƙushe wannan matsalar ba?

• A yanzu wane mataki ka ɗauka don ganin ka gina ma kanka 'capacity' ta wannan ɓangaren?

MU MATASA NE, ko? Bari na ba da wani misalin da wataƙila za a fi gane wa:

A lokacin da kake soyayya da ASIYA, tsawon shekara 2 ba wata tsayayyar magana. Ba kuma wani abu ne ya saka kake tsoron shigo da maganar aure ba face maganar rashin kuɗi. Rashin kuɗi shi ne rauninka (weakness).

Kwatsam! Babanta ya ce ka fito, saboda akwai wani ɗan gidan kawunta da ya nuna yana son ta ita kuma ta ce sai kai, kai ta zaɓa, kai take so. Sai ka ce ba ka da halin aure a yanzu, Baban Asiya ya ce, ai kuwa sai dai ka haƙura, Asiya ba za ta tsaya jiranka ba don ta fara girma, shekaru 2 tana jira! Sam ba zai iyu ba.

Kana ji, kana gani har IV na aurenta Asiya ta aiko maka. Asiya ta yi aure, an sha biki, ta tafi ta bar ka da 'heartbreak'. Ka ɓata shekara 2 a banza.

Me ya jawo maka wannan damuwar? Weakness ɗinka ne na rashin kuɗi, ba wai don ba ka son Asiya ba.

Me kake yi tsawon shekara 2 a baya don yaƙar wannan 'weakness' naka? A yanzu kuma wane shiri za ka fara don kada abin da ya faru da ASIYA ya sake faruwa da duk wata yarinyar da za ka tsayar da sunan soyayya?

PROACTIVISM na nufin yin kataɓus ɗin nemo hanyoyi magance matsaloli maimakon zama da matsalar tsawon lokaci, domin kada ka zauna kana ƙorafi.

Misali, a lokacin da kake jin yunwa, ai ba zama ka yi kana ta maimaita cewa "ina jin yunwa", "ina jin yunwa"... ba; a'a, tashi ka yi ka je nemo abinci, da daɗi ko ba daɗi ka ci domin ka kashe wannan yunwar. Ba zauna wa ka yi ka bari yunwa ta kashe ka ba.

Za ka iya zama PROACTIVIST ma rayuwarka domin magance 'weakness(es)' naka? 

Wane yunƙuri za ka yi don nemawa kanka mafita ta aiki domin dogaro da kanka da samun kuɗin kashewa maimakon dogara da wani ko jiran tsammani?

Wane mataki za ka ɗaukar ma kanka kan ƙunci da ɓacin rai da fargaba da yarinyar can da kake so take saka ka, kullum kana cikin zulumi?

A duk lokacin da ka ji jinya, Shari'a ta ce ka nemi magani na wannan jinyar. A lokacin da kafiran Makkah suka matsawa Manzon Allah ﷺ tare da sauran Sahabansa, sai Ubangiji ya umarce su da su yi hijri, su bar Makkah. WANNAN SHI NE PROACTIVE MEASURE, maimakon zama cikin takura, an nemi mafita.

IDAN BA CANJA BA, BABU ABIN DA ZAI CANJA A RAYAWARKA, ABOKINA! Ƙorafi da surutu ba su canja komai, wannan shi ƙa'idar rayuwa.

إن الله لا يغير ما بقوم حتى يغيروا ما بأنفسهم

✍🏻Aliyu M. Ahmad
9th Shawwal, 1445AH
18th April, 2024CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
#AliyusDosage #AliyusWriteups #MorningDosage #AliyuProactivist 

Post a Comment

0 Comments