Social media ta zo da alkhairai masu yawa, amma ta wata fuskar kuma, akwai sharri, shi ma mai yawa. Daga cikin illolin 'social media' akwai yaɗuwar alfasha. Kallon 'bat*a' (po*n) a media ya shafi mutane da dama (har mutanen kirki), sai dai wanda Allah ya tseratar [Yusuf, aya ta 53].
Shawarar da zan bawa ma'aboci kallon alfasha (batsa/po*n) a yanar gizo:
1. Kai tsaye, kallon hotuna, bidiyo ko karanta wallafar dake tayar da hankali (erotic contents) a 'media' ko 'zahiri' haramun ne. Umarni ne daga Ubangiji ﷻ, cewa; "a faɗawa mummunai maza da mata, su riƙa runtse idanuwansu, su kuma kiyaye al'aurarsu" [AnNur, aya ta 30].
2. Duk aiyukan da gaɓɓan jikinka suka aikatawa, da 'ji' (da kunne) da 'gani' (da ido) da abin da zuciya (tunane-tunane) ke ƙullawa, za a tuhume ka a kansu, a ranar Alkiyama [Al-Isra', aya ta 36].
3. Kallo batsa (po*n) yana da wuyar dainawa idan ya zamewa mutum jiki (addiction), har ga masu aure; saboda fitina ce. Shi yasa Ubangiji ﷻ ya yi mana gargaɗi da cewa, "kar mu kusanci zina" [Al-Isra', aya ta 32]. "Kada mu kusanci alfasha, wacce ta bayyana da wacce take a ɓoye..." [Al-Anam, aya ta 151].
4. Kallon batsa (po*n) ZINA NE. Zina ɓata taƙaita a iya haɗuwar 'namiji' da 'mace' ba; sauran gaɓɓan jiki ma suna zina. Zinar ido, ta ce kallon haram (tsiraici/batsa). Zinar harshe, ita ce zantukan batsa... farji ke gaskata hakan ko ya ƙaryata [Bukhari, 5889].
Kuma, yawaita kallo ko sauraro 'batsa (po*n), ya kan ja mutum zuwa ga aikata babbar zina, ko istimna'i (zinar hannu/masturbation), da sauransu [Sahih Muslim, 2657].
5. Ka ji tsoron Allah ﷻ a duk inda kake. Ko da ka ɓoye/ɓuya a wani waje, ko ka goge 'history' don kar mutane su sani; mu sani, duk abin da muke Allah ﷻ ya sane da abin da muke aikatawa [Jami' al-Tirmidhi, 2115].
6. Idan 'social media' za ta zame ma fitina, barin amfani da ita ɗin shi ne ya fi ma alheri. Ka yi ƙoƙarin kaucewa duk shafukan da suke yaɗawa alfasha, ta hotuna, bidiyo ko rubutu, ko raye-rayen batsa. Kallo batsa masifa ne, koda aure mutum ya yi, yana da wuya ya daina, matuƙar ya zame masa jiki (addicted).
Allah Ya tsare mu daga afwaka zina ta kowacce fuska; gani, ji... Allah Ya shiryar mana da zuri'a.
✍️ Aliyu M. Ahmad
9th Shawwal, 1443AH
10th May, 2022CE
#AliyuMAhmad #SocialMedia #FasaharZamani

0 Comments