Elite vs. Influencer


A nazarce, ba wata kalma ELITE a social media, sai dai INFLUENCER.

------------------------------
* Shiga 👉👉 https://bit.ly/ElitedaInfluencer domin karanta cikakken rubutu game da SOCIAL MEDIA INFLUENCER
------------------------------

Influencer shi ne mutum mai tarin mabiya a social media (followers), influencer ya karkasu zuwa yawan followers: mega (1m+), macro (40k – 1m), micro (1k – 40k), nano (mai followers kasa da 1k).

Elite a nazariyyar zamantakewa (sociological theory), rukuni ne na mutumin da suke riƙe da madafun iko (mulki), ko tarin dukiya. Ana auna matsayin mutum a ‘elite class’ da dukiya ko iko ne a rayuwar zahiri.

Zama influence a social media ba ya buƙatar kasancewa cikin rukunin ‘elite’ a zahiri, domin zuwan social media ya ɗaga darajar waɗanda ba kowa ba, zuwa sanannu, saboda bayyanar wata baiwa da Ubangiji ya musu. Mai buƙatar ‘contents’ da kake wallafawa, zai bibiye ka.

Akan sami ‘elite’ influencer a social media (kamar ‘yan siyasa, malamai, mawaƙa, ‘yan film...), akan kuma sami waɗanda suke rukunin elite amma ba shi da influencing a social media. Sai dai ta ɓangaren halayya, wani lokacin, influencer na nuna irin halin elite, “privileging”, ma’ana, nuna tausasawa da kulawa ga influencers ‘kwarya ta bi kwarya’ a alakar social media.

✍️ Aliyu M. Ahmad
8th Safar, 1444AH
5th September, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
#FasaharZamani
#Influencer


Post a Comment

0 Comments